Kano: Sarakunan Gaya, Karaye, Bichi da Rano sun shiga cikin doka

Kano: Sarakunan Gaya, Karaye, Bichi da Rano sun shiga cikin doka

Dazu nan Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sa hannunsa a kan dokar nan da ta jawo ce-ce-ku-ce a kan raba masarautar kasar Kano da aka yi zuwa gidaje 5.

Daily Nigerian ta rahoto cewa gwamnan ya sa hannu a wannan kudiri da majalisa ta amince da shi dazu a matsayin doka. A Ranar 5 ga Watan Disamban 2019, majalisa ta yi na’am da kudirin.

A farkon Watan Mayun 2019, gwamnatin Abdullahi Ganduje ta rattaba hannu a kan dokar da ta kirkiro wasu sababbin Masarautu hudu a cikin jihar Kano; Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya.

Sai dai bayan fiye da watanni shida da nada wadannan Sarakuna sai kotu ta ruguza nadin na su. A wani hukunci, babban kotun jihar Kano ya wargaza duka wadannan Masarautu da aka kafa.

KU KARANTA:

Bayan wannan hukunci ne, a cikin ‘yan kwanakin nan, Abdullahi Ganduje ya sake dumfarar majalisar dokokin Kano da wani sabon kudiri, inda ya hakikance a kan barka Masarautun jihar.

A Ranar Alhamis, ‘yan majalisa su ka amince da kudirin bayan ya tsallake matakan sauraro a zauren majalisar. Majalisar ta amince da kudirin ne ba tare da ta yi wasu garambawul ba.

Kamar yadda Jaridar ta rahoto, sashe na 12 na wannan kudiri ne kurum majalisar ta yi wa kwaskwarima, inda aka ce dole gwamna ya nemi iznin majalisa game da taba darajar Sarakuna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel