Ba a taba biya na ko kwabo ba na fansho a matsayina na tsohon gwamna - Amaechi

Ba a taba biya na ko kwabo ba na fansho a matsayina na tsohon gwamna - Amaechi

Ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Ameachi ya yi martani kan hukuncin da kotun tarayya ta yanke inda ta bawa gwamnatin tarayya umurnin karbo dukkan kudaden fansho da allawus da tsaffin gwamnonin jihohi da suka zama sanatoci suka karba.

LIB ta ruwaito a baya cewa Kungiyar kare hakkin al'umma, SERAP, ta samu nasara a kotu inda ta shigar da kara ta nemi a karbo kudi kimanin naira biliyan 40 da tsaffin gwamnoni suka karba duk da cewa yanzu sun zama sanatoci da ministoci.

Wadanda aka yi ikirarin abin ya shafa sun hada da Bukola Saraki, Godswill Akpabio Rabiu Kwankwaso, Theodore Orji, Abdullahi Adamu, Sam Egwu, Shaaba Lafiagi, Joshua Dariye, Jonah Jang, Ahmed Sani Yarima, Danjuma Goje, Bukar Abba Ibrahim, Adamu Aliero, George Akume, Biodun Olujimi, Enyinaya Harcourt Abaribe, Rotimi Amaechi, Kayode Fayemi, Chris Ngige da Babatunde Fashola.

Sai dai a martanin da ya yi game da hukuncin kotun, Rotimi Amaechi da aka ambaci sunansa cikin jerin wadanda suka amfana da fanshon ya musanta cewa ya taba karbar fansho a matsayinsa na tsohon gwamna tun bayan da ya sauka daga mulki a 2015.

DUBA WANNAN: Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

Ya kara da cewa idan da an bashi kudin ma, zai mayar da kudin ne ya bukaci ayi amfani da shi wurin biyan ma'aikatan jihar Rivers fansho.

Ga sakon da ya wallafa a Twitter: "Ban taba neman a bani ko kwabo ba a matsayin fansho daga gwamnatin jihar Rivers. Idan da an bani, zan mayar musu in bukaci ayi amfani da kudin a biya ma'aikatan jihar fansho.

"Ban amince in rika karbar fansho a matsayin tsohon gwamnan jihar Rivers ba yayin da ina rike mukamin minister".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel