INEC ta tsayar da ranar maimaita zabukka 28 da kotu ta soke

INEC ta tsayar da ranar maimaita zabukka 28 da kotu ta soke

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace kotu ta bada umarnin maimaicin zabe da zaben cike gurbi 30 amma 2 kacal ta yi a cikinsu a fadin kasar nan.

Hukumar ta ce, bayan duba wasu lamurran da ke zagaye da canza zabukan, wadanda suka hada da lokacin da hukumar zata shirya, bayanan inda za a canza zaben, shigowar lokacin bikin kirsimati da sauransu. Hukumar ta yanke hukuncin maimaita zabukan nan da ranar Asabar, 25 ga watan Janairu, 2020.

Shugaban kwamitin bayanai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ya sanar da hakan a ranar Alhamis a Abuja taron hukumar kashi na 51.

Yace anyi taron ne don tattauna yadda za a maimaita zabukan bayan korafin jama'a da kotu ta saurara a 2019. Za a fitar da bayanai dalla-dalla nan ba da dadewa ba.

DUBA WANNAN: Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

"A hukuncin kotu, ta bukaci maimaita zabuka 30. Biyu daga ciki ne kadai aka samu aka yi a ranar 30 ga watan Nuwamba 2019."

"A halin yanzu, akwai umarnin kotu 28 da ba a cika ba a jihohi 12 a fadin kasar nan. Bayanan sun hada da kujerar sanata daya, kujerar majalisar wakilai 12 da majalisar jihohi 15," Okoye ya ce.

Kamar yadda ya ce, sau da yawa zabukan za a maimaitasu a mazabu ne kadai kuma hukumar zata fitar da bayanan inda yankunan da abun ya shafa.

Yace, biyo bayan zaben 2019, an samu koke 807 da aka shigar a kotun sauraron kararrakin zabe daban-daban, an kori 582 daga ciki inda aka janye 183 daga ciki.

"Daga cikin ragowar 42 din, kotun sauraron kararrakin zaben ta umarci canza zabe 30 daga ciki tare da bada umarnin bada shahadar komawa kujera ga 12 daga ciki," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel