Dan Allah kada ku sa min ankwa - Orji Kalu ya roki ganduroba yayinda za'a tafi dashi gidan yari

Dan Allah kada ku sa min ankwa - Orji Kalu ya roki ganduroba yayinda za'a tafi dashi gidan yari

Yayinda ake shirin awon gaba da shi zuwa gidan gyara hali, an ji Orji Uzor Kalu yana rokon jami'an hukumar gidajen gyara hali su taimaka kada su sanya mai ankwa.

Kotu ta yankewa Tsohon gwamnan jihar Abiya hukuncin gidan yarin shekara 12 kan laifin almundahanan bilyan bakwai.

Orji Kalu a yanzu shine mai tabbatar da ladabi a majalisar dattawan Najeriya.

Yayinda ake fitar da Orji Kalu da abokan laifinsa daga cikin akwatin mai laifi a kotu, gandurobobi sun yi kokarin sanya masa ankwa.

A lokacin yace: "Ina za ku kaimu yanzu? Dan Allah kada ku sanya min ankwa, zan bi ku."

An hango wasu mutane biyu suna kwarara hawaye yayinda akayi gaba da Kalu.

Alkalin Kotun, Jastis Idris Mohammed ya yankewa abokin laifin Kalu, Udeogu, hukuncin shekaru 10 a kurkuku yayinda ya bada umurnin sadaukarwa gwamnati kamfanin Slok Limited, mallakar Kalu.

Dan Allah kada ku sa min ankwa - Orji Kalu ya roki ganduroba yayinda za'a tafi dashi gidan yari
Orji Kalu ya roki ganduroba yayinda za'a tafi dashi gidan yari
Asali: Twitter

Dan Allah kada ku sa min ankwa - Orji Kalu ya roki ganduroba yayinda za'a tafi dashi gidan yari
Dan Allah kada ku sa min ankwa - Orji Kalu ya roki ganduroba yayinda za'a tafi dashi gidan yari
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel