Yanzu-yanzu: Bayan hukuncin Orji Kanu, Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin APC

Yanzu-yanzu: Bayan hukuncin Orji Kanu, Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin APC

Bayan hukuncin kotun da ta yanke jefa babban sanatan APC kurkukun shekaru 12, shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a fadar Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.

Wadanda ke cikin ganawar tare da Buhari sune mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

An kaddamar da ganawar ne misalin karfe 3 na rana kuma suna ciki yayinda muke kawo wannan rahoton, inji The Nation.

Gwamnonin da ke hallare sune gwamnonin Osun, Ogun, Plateau, Kebbi, Niger, Jigawa,Ekiti, Kaduna, Nasarawa, Borno, da Edo.

Gwamnan jihar Kogi ya samu wakilcin mataimakinsa, Edward Onoja.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel