Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya shiga majalisar dattawa

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya shiga majalisar dattawa

Tsohon dan takarar shugabancin Najeriya, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya dira majalisar dattawan Najeriya da safiyar Alhamis, 5 ga watan Disamba.

Jaridar Punch ta ruwaito Atiku ya tafi majalisar dattawan ne domin halartar zaman sauraron korafe korafen jama’a game da kudurin sauya jami’ar kimiyya ta Modibbo Adama dake jahar Adamawa zuwa jami’ar komai da ruwanka.

KU KARANTA: Zaratan Sojojin Najeriya sun karkashe yan Boko Haram, sun ceto mutane da dama

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya shiga majalisar dattawa

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya shiga majalisar dattawa
Source: Facebook

An gudanar da wannan zama ne a dakin taro na 231 dake cikin majalisar dattawan, kuma Atikun ya halarci zaman ne a matsayinsa na dan jahar Adamawa, mai kishin jaharsa kuma mai ruwa da tsaki a harkar ilimi.

Idan za’a tuna, a ranar 25 ga watan Nuwamba ne Alhaji Atiku Abubakar ya dawo Najeriya bayan kwashe kimanin watanni 5 yana hutawa a kasar Dubai yana hutawa tare da gudanar da sha’aninsa daban daban.

Tun a watan Maris Atiku ya fice daga Najeriya bayan shan kaye a zaben shugaban kasa wanda ya gudana a watan Feburairun 2019, zaben daya kalubalanta har zuwa kotun koli, wanda daga karshe ta tabbatar da shugaba Buhari a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben.

Bugu da kari, ranar 25 ga watan Nuwamba ne ya yi daidai da ranar haihuwar tsohon mataimakin shugaban kasan, sai dai ba a yi wani shagalin bikin murnar cikarsa shekaru 73 ba, kamar yadda ya bukata.

Ko a ranar murnar zagayowar ranar haihuwarsa na shekarar da ta gabata, Atiku ya dakatar da danginsa, yan uwa da abokansa na arziki daga shirya masa wani shagalin biki, inda ya nemi su sadaukar da duk kudin da za su kashe wajen shagalin ga gidajen marayu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel