Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin tarayya ta tabbatar da kasafin kudin 2020, ta kara N300bn

Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin tarayya ta tabbatar da kasafin kudin 2020, ta kara N300bn

Yan Majalisar dokokin tarayya sun tabbatar da kasafin kudin da shugaba Buhari ya gabatar a ranar 5 ga Disamba, 2019.

Yan majalisan sun tabbatar da kasafin kudin ne bayan kimanin kwanaki arba'in da shugaban kasa ya gabatar da takardan gabansu.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Sanata Barau Jibrin, ya kawo kasafin majalisa bayan kwamitinsa ta kammala bincikenta.

Yan majalisun sun kara kudin da Buhari ya gabatar daga N10.33 trillion zuwa N10.6 trillion (10,594,362,364,830).

A jawabinsa, Barau Jibrin ya bayyana cewa bisa lissafin hakar gangan mai milyan 2.18 a rana, sun mayar da farashin kowani gangan zuwa $57 daga $55 da Buhari ya gabatar; sun kara $2.

A ranar Talata, 8 ga watan Oktoba, 2019 shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin Najeriya ta shekarar 2012 ga majalisar dokokin tarayya.

Ga kiyasin da aka gina kasafin kudin kai da hotunan taron:

Danyen man da za'a rika haka a rana: Ganga milyan 2.18

Farashin kowani Ganga daya a : $57

Farashin Dala: N305 / $

Kudin shigan da ake sa ran samu a shekerar 2020:

Dagar arzikin Man fetur : 2.64 trillion

Arzikin Sabanin Mai (Haraji) : 1.81 trillion

Sauran hanyoyi ( sauransu) : 3.7 Trillion

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel