Da duminsa: Kotu ta yanke wa tsohon gwamna, Sanata Orji Kalu, hukuncin daurin shekaru 12

Da duminsa: Kotu ta yanke wa tsohon gwamna, Sanata Orji Kalu, hukuncin daurin shekaru 12

Wata babbar kotun tarayya a jihar Legas, a ranar Alhamis ta yankewa sanata kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu, shekaru 12 a gidan gyaran hali. Ta kamashi dumu-dumu ne da damfarar N7.65bn.

Jastis Mohammed Idris wanda ya yanke wannan hukuncin, ya bayyana cewa an kama sanatan da laifin ne don kusan shekaru 12 kenan da ake shari’ar.

An gurfanar da Kalu ne tare da kamfanin Slok Nigeria Limited tare da Udeh Udeogu, wanda shine daraktan kudade da asusun gidan gwamnatin jihar Abia yayin mulkin Kalu.

A cikin tuhume - tuhume 39 da hukumar EFCC ke yi musu, an zarge su da hada baki tare domin karkatar da biliyan daga asusun jihar Abiya.

A daya daga cikin tuhumar da ake yi musu, EFCC ta yi zargin cewa Mista Kalu, wanda ya kasance gwamnan jihar Abiya daga shearar 1999 zuwa 2007, da yin amfani da wani kamfani, "Slok Nigeria Limited", wanda mallakarsa ne wajen karkatar da adadin kudaden.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Majalisar jihar Kano ta amince da kudirin karin masarautu a jihar Kano

Masu gabatar da kara sun yi ikirarin cewa an yi amfani da asusun bankuna da yawa wajen juya kudaden domin samun saukin karkatar da su daga asusun gwamnatin jihar zuwa asusun kamfanin.

Lauya mai gabatar da kara, Rotimi Jacoobs, ya ce tsohon gwamnan ya saba wa sashe na 17(c) na dokar haramta safarar kudi ta shekarar 2004, wacce aka tanadar wa hukunci a sashe na 16 na kundin dokar.

Bayan biliyan N7.1 da ake zargin ya karkatar, EFCC na tuhumar tsohon gwamnan tare da sauran wadanda aka gurfanar da karbar jimillar miliyan N460 da ake zargin cewa an sace su ne daga asusun gwamnatin jihar Abiya a tsakanin watan Yuli zuwa Disamba na shekarar 2002.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel