Yanzu-yanzu: Kotu ta ba DSS sa'o'i 24 ta saki Sowore

Yanzu-yanzu: Kotu ta ba DSS sa'o'i 24 ta saki Sowore

Babbar kotun tarayyan dake zaune a Abuja ta baiwa hukumar DSS sa'o'i 24 ta saki shugaban jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore.

Alkali mai shari'ar, Jastis Ijeoma Ojukwu, wacce ta bada umurnin ta ci tarar hukumar DSS N100,000 kan jinkirin sakinsa.

Alkalin wacce ta nuna bacin ranta abinda DSS tayi kuma haka ya kai ga dage karar har sai an biya Soworw kudin.

An dage karar zuwa ranan 6 ga Disamba, 2019.

Yanzu-yanzu: Kotu ta ba DSS sa'o'i 24 ta saki Sowore

Yanzu-yanzu: Kotu ta ba DSS sa'o'i 24 ta saki Sowore
Source: Original

A baya, Hukumar Jami'an tsaro na farin kaya (DSS) ta yi ikirarin cewa a shirye ta ke ta saki dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zaben 2019 kuma mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore sai dai wadanda suka zo karbarsa ne ba su cancanta ba.

Hukumar ta yi wannan jawabin ne ta bakin mai magana da yawunta, Peter Afunaya ya fadi a ranar Laraba kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Afunaya ya kuma karyata cewa jami'an hukumar sun bude wa masu zanga-zanga wuta a ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel