Yanzu-yanzu: Kotu ta kama Sanata Uzor Kalu na APC da laifin satar almundahanar N7.2bn

Yanzu-yanzu: Kotu ta kama Sanata Uzor Kalu na APC da laifin satar almundahanar N7.2bn

Babbar kotun tarayya dake zaune a jihar Legas ta kama tsohon gwamnan jihar Abiya kuma bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, da laifin almundahanar N7.2bn.

Shekaru 12 kenan hukumar EFCC ta ke tuhumar tsohon gwamnan tare da wani kamfaninsa, Slok Nigeria Limited, da kuma tsohon Daraktan kudi kuma akanta na gwamnatinsa, Jones Udeogu.

Tsawon wannan shekaru 12, Orji Kalu, ya kasance yana karyata zargin da EFCC ke masa wanda ya kai ga yiwa jihar gori a wani lokaci.

A watan Agusta, Orji Kalu ya gabatar da jawabai na kare kai, inda yace "Jihar Abia ba ta da wannan arzikin, kuma ko a lokacin da zan sauka daga mulki, sai da muka ci bashi kafin mu iya biyan albashin ma'aikata."

"Dudu-du a lokacin da muka karbi jagoranci a watan Yunin 1999, abin da jihar Abia ke samu daga gwamnatin tarayya a kowane wata bai wuce naira miliyan 168 zuwa 172."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel