Abin da mamaki: An ciro almakashin tiyata da ya shekara 18 a cikin wani mutumi

Abin da mamaki: An ciro almakashin tiyata da ya shekara 18 a cikin wani mutumi

- Bayan shekaru 18 da yi wa wani mutum dan kasar Vietnam tiyata, an sake wata inda aka ciro almakashi

- Bayan kammala waccan tiyatar ta farko, likitocin sun manta da almakashi mai tsawon inci 6 a cikinshi

- A halin yanzu ma’aikatar lafiyar lardin na neman likitan da yayi wannan aika-aikar don fuskantar hukunci

Bayan shekaru 18 da yi wa wani mutum dan kasar Vietnam tiyata a wani asibiti, likitoci sun yi nasarar ciro almakashin da wadancan likitocin suka manta a cikinshi a tiyatar baya. An yi wa mutumin aikin ne saboda yawan ciwon cikin da ke damunshi.

Mara lafiyan mai suna Ma Ban Nhat, wanda yanzu yake da shekaru 54 a duniya, an yi mishi tiyata ne bayan da ya yi hadarin mota. Bayan bincike ya tsananta ne aka gano cewa akwai karfe a cikinshi.

Ma Ban Nhat, yace likitocin sun tuna da almakashin ne bayan sun yi mishi dinki. A karshen makon jiya ne kuma aka yi nasarar cire mishi almakashin.

An gano da almakashin ne bayan da aka yi masa hoton cikin. Almakashin ya kai tsawon inci 6, kuma tiyatar fitar dashi din ta dau awa hudu kafin a samu nasarar cireshi.

KU KARANTA: Budurwa tayi kokarin kashe kanta domin ta dorawa saurayinta laifi saboda ya rabu da ita

Mataimakin shugaban gudanarwa ma Asibitin Gang Thep Thai Nguyen da ke da nisan mil daya da Arewacin garin Hanoi, Mista Ngo Trung Thang, ya sanar da kafar yada labarai ta AFP cewa, Ma Ban yana samun sauki, bayan ya kai kimanin shekaru 20 yana ci da sha kuma almakashin na cikin shi.

Kamar yadda kafar yada labarai ta Suc Khoe ba Doi Song ta wallafa, a halin yanzu jami’an ma’aikatar lafiya na kasar na neman likitan da ya manta da almakashin tun 1998 a lardin Bac Kan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel