Yanzu-yanzu: Bututun mai ya fashe a jihar Legas, akalla mutum 1 ya hallaka

Yanzu-yanzu: Bututun mai ya fashe a jihar Legas, akalla mutum 1 ya hallaka

Bututun mai ya fashe da a jihar Legas da sassafen nan a unguwar Diamond Estate, Isheri Olofin, karamar hukumar Egbe-Idimu ta jihar.

Bidiyon da ya bayyana a kafafen sadarwa ya nuna yadda unguwar ke ci bal-bal kuma mutane suna guduwa domin ceton rayuwarsu.

Har yanzu ba'a san abinda ya haddasa fashewar bututun man ba amma mazauna unguwar sun bayyana cewa matasa masu kokarin satar mai ne suka haddasa.

Har yanzu ba'a san iyakan wadanda ya shafa ba amma kawo yanzu mutum daya ya mutu.

Hukumar agaji na gaggawan jihar Legas sun garzaya wajen kuma jami'an kwana-kwana sun kashe wutar.

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel