Idan bamu kawo karshen almajiranci ba, za ta zaman mana kaska - FG

Idan bamu kawo karshen almajiranci ba, za ta zaman mana kaska - FG

Mai bada shawara kan lamuran tsaron kasa, Babagana Munguno, ya ce gwamnati ba za ta cigaba da jinkiri wajen kawar da almajiranci ba a Najeriya.

Yayinda yake magana a taron kaddamar da sabon salon tabbatar da tsaro a Najeriya ranar Laraba, Babagana Munguno, ya ce idan ba'a kawo karshen almajiranci ba, "za ta zamar mana babbar matsala"

A watan Yuni, Munguno ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shawaran haramta almajiranci domin tabbatar da cewa babu yaron da aka hana samun ingantaccen ilimi.

Yace:"Lamarin Ilimi na jingine da hana yara zuwa makaranta, wannan almajirancin da kua dade muna magana akai, ba zai yiwu mu cigaba da jinikiri wajen maganceshi ba saboda zai dawo ya zame mana kaskar da bamu tunani."

"Ya kamata mu dakile wannan abun kuma hakkinmu ne gaba daya mu kula da hakan ba tare da wani tsoro ba."

Ya ce lamarin rashin tsaron Najeriya na samun zagon kasa daga kasashen waje, rikice-rikicen cikin gida da waje ne ya zaman mana katutu da hadaru ga rayukanmu gaba daya.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel