Yan bindigan Zamfara da Katsina sun tare a jihar Neja - Sanatoci

Yan bindigan Zamfara da Katsina sun tare a jihar Neja - Sanatoci

A ranar Laraba, Sanatocin jihar Neja sun bayyana cewa yan bindigan jihar Katsina da Zamfara sun tare a jihar Neja kuma sun addabi al'ummar jihar.

Sanata Sani Musa mai wakiltan Neja ta gabas ya ce yan bindigan suna cin karansu ba babbaka a wasu sassan jihar.

Ya ce an yi garkuwa da masu unguwanni biyu inda suka kai hari garuruwan suka kashe na kashewa kuma da dama sun jikkata.

"Za ku yi mamakin mutanen da na gani, da wuya su rayu saboda irin raunukan harsasan da suka samu." A cewarsa

Sanata mai wakiltar Neja ta Arewa, Sabi Abdulli ya bayyana cewa yan bindigan jihar Katsina da Zamfara sun tare a jihar Neja.

Ya yi kira ga majalisar ta san nayi domin dakile wadannan yan ta'addan.

Majalisar dattawar ta yi kira ga hafsoshin hukumar Soji da sifeto janar na hukumar yan sandan su tura jami'ansu wuraren da ya shafa a jihar Neja.

Hakazalika ta yi kira ga hukumar bada agaji na gargajiya ta samar kayayyakin tallafi ga mutanen da hare-haren ya shafa a jihar Neja.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel