Rashin wutar lantarki ya hana zaman kotu a Abuja

Rashin wutar lantarki ya hana zaman kotu a Abuja

Peter Kekemeke, alkali ne a babbar kotun birnin tarayya, Abuja, ya yanke sauraron kowacce kara a kotun a ranar Laraba saboda rashin wuta da ya gallabi kotun a jiya.

Akwai a kalla shari'a 11 da za a saurara a jiya Laraba, amma aka dakatar da sauraron.

Wadanda suka bayyana a kotun sun hada da shaidu da lauyoyi, duk sun hallara a dakin kotun da karfe 8:30 na safe don jiran fara zaman kotun da karfe 9 na safe.

Amma Kekemeke ya hallara kotun ne mintoci kadan bayan karfe takwas. Ya samu kotun da duhu. Jim kadan bayan isarsa, ya sanar da cewa babu zaman kotu saboda matsalar rashin wuta.

DUBA WANNAN: Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

"Ya nuna cewa ba zamu iya zaman kotu ba a yau. Ma'aikatana sun sanar dani babu wutar lantarki saboda matsalar da aka samu da kamfanin rarrabe wutar lantarki na Abuja," in ji shi.

"Wannan kuma, babu fetur da zamu tada injin samar da wuta. A bayyane yake cewa dole ne mu sanya wata rana don dawowa lokacin da aka shawo kan matsalar wutar."

Lauyoyi da yawa sun nuna rashin jin dadinsu a kan lamarin kuma sun dora laifi a kan hukumar shari'a ta birnin tarayya a kan wannan halin da suke nunawa.

Wasu daga cikin lauyoyin sun ce, sun hallara a kotun ne bayan doguwar tafiyar da suka yi. Sun kuma biya kudin masauki don samun hallara a kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel