Majalisa ta yi kira ga Buhari ya gudanar da kidayar yan Najeriya a 2020

Majalisa ta yi kira ga Buhari ya gudanar da kidayar yan Najeriya a 2020

Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari daya shirya kidayar yan Najeriya zuwa shekarar 2020 domin sanin takamaime kuma sahihin adadin yan Najeriya, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar na cewa sakamakon kidayar da aka yi a shekarar 2006 bashi da wani tasiri a yanzu musamman wajen yin tsare tsaren cigaba ga yan Najeriya sakamakon karuwar jama’a da aka samu daga lokacin zuwa yanzu.

KU KARANTA: Kafa sabbin masarautu: Ganduje ya fasa majalisar dokokin jahar Kano gida biyu

Dan majalisan jam’iyyar APC daga jahar Legas, Ademorin Kuye ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar, inda yace idan har ba an mayar da kidayar yan Najeriya wajibi kamar yadda ake gudanar da zabe ba, haka za’a cigaba da daukan tsawon lokaci ba tare da an san san yawan jama’a ba.

“Da alkalumman kidayar jama’a ne kadai gwamnati za ta san adadin yaran da ake haihuwa a kasar, yawan makarantun da ake bukata, yawan asibitocin da ake bukata, yawan ma’aikatan dake garuruwanmu da kuma yawan baki yan kasashen waje dake kasar, duk domin a shirya ma ababen more rayuwa daya kamata a samu a kasar.

“Tattalin arzikin Najeriya na sauyawa, ga shi kuma kasar na da dimbin al’umma da ake sa ran yawansu zai rubanya a nan da shekaru 20 masu zuwa, don haka kidaya nada muhimmanci wajen cigaban kasa wanda ta haka ne za’a samu bayanan da ake bukata don samar da cigaba.” Inji shi.

Dan majalisan ya kara da cewa kamata yayi a dinga gudanar da kidaya bayan shekaru goma, amma a baya hakan bai yiwu ba saboda wasu dalilai na siyasa, dalilan tsaro ko kuma matsalar rashin kudi.

Sai dai ko a shekarar 2006 da aka gudanar da kidayar, kotuna da dama sun soke sakamakon kidaya na wurare da dama sakamakon rashin sahihancinsu saboda an siyasantar da aiki, da kuma aringizon alkalumma.

Daga karshe majalisar ta bukaci hukumar kidaya ta kasa da ta samar da jadawalin da za’a iya dabbakawa wajen gudanar da aikin kidayar jama’an yan Najeriya a shekarar 2020.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel