Rufe iyakokin Najeriya: Kwastam ta kama jarkokin man fetir 19 a cikin akwatunan gawa

Rufe iyakokin Najeriya: Kwastam ta kama jarkokin man fetir 19 a cikin akwatunan gawa

Hukumar kwastam ta dakile yunkurin wasu yan fasa kauri a lokacin da suka yi kokarin haurawa da jarkokin man fetir guda 19 wanda suke boyesu a cikin wasu akwatunan gawa guda biyu a kan iyakar Najeriya da kasar Bini.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa jami’an hadaka dake yaki da masu fasa bututun mai na hukumar ne suka samu nasarar kama kayan a iyakar Idiroko dake jahar Ogun.

KU KARANTA: Kafa sabbin masarautu: Ganduje ya fasa majalisar dokokin jahar Kano gida biyu

Rufe iyakokin Najeriya: Kwastam ta kama jarkokin man fetir 19 a cikin akwatunan gawa

Rufe iyakokin Najeriya: Kwastam ta kama jarkokin man fetir 19 a cikin akwatunan gawa
Source: UGC

Kaakakin hukumar kwastam na yankin, Abdullahi Maiwada yace yan fasa kaurin sun jefar da motar dake dauke da kayan ne, wanda daga bisani bincike ya nuna an zuba jarkoki guda 19 makare da man fetir a cikin wasu akwatunan gawa guda 2 a cikin motar.

“A kokarinmu na cigaba da yaki da fasa kauri, jami’an hukumar kwastam na shiyyar Ogun sun kama jarkoki 13 masu lita 25 da kuma jarkoki 6 masu lita 10 dukkaninsu cike da man fetir da aka boyesu a cikin wasu akwatunan gawa guda biyu.

“Wani sanannen dan fasa kauri ne ya dauko wadannan kaya da nufin haurawa dasu kasar Bini a cikin wata mota kirar Mazda 626 mai lamban Legas Da wannan rundunar take jaddada manufarta na ba gudu babu ja da baya wajen yaki da fasa kauri.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Abdullahi ya yi kira ga yan Najeriya dasu rungumi halastattun hanyoyi wajen neman halaliyarsu tare da kauce ma bin munana hanyoyin fasa kauri domin kuwa rundunarsu ba za ta saurara ma duk masu cin amanar kasa ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata sabuwar tsarin gudanar da tsaro a Najeriya da gwamnatinsa ta kirkira, mai taken “Dawo da tsaro a Najeriya”.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da sabon tsare tsaren ne a wani taro daya gudana a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, jim kadan kafin fara taron majalisar zartarwa.

Manufar wannan sabuwar tsari shi ne don shawo kan babbar kalubalen matsalar tsari da ta dabaibaye najeriya, a jawabinsa, shugaba Buhari yace an samar da tsare tsaren ne bayan tattaunawa tare da tuntuba tsakanin dukkanin hukumomin tsaron Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel