Boko Haram: An kera wasu motocin yakin MRAPs a cikin Najeriya

Boko Haram: An kera wasu motocin yakin MRAPs a cikin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu ya kaddamar da wasu motocin da aka kera a Najeriya domin yakin Boko Haram. An kaddamar da wadannan motoci ne a Ranar Talata, 4 ga Watan Disamban 2019.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust, kamfanin Sojin Najeriya na DICON tare da hadin gwiwar sashen CED na Injiniyoyin gidan Sojan kasar ne su ka kera wadannan motoci.

Dakarun sun kera motar nan da ake kira MRAP wanda ba ta jin bam ne saboda shiga yankin Boko Haram. Wannan ya na cikin kokarin kawo karshen Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Za a fara amfani da wadannan motocin yaki ne a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya inda ‘Yan Boko Haram su ka dade su na ta’adi. Shekaru fiye da goma kenan ana yaki da ta’addaci.

KU KARANTA: Ashe Jahilai sun kusa fara mulki a Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari shi ne ya kaddamar da wadannan motoci na musamman a wajen taron da shugabann hafsun sojin Najeriya ya shirya na wannan shekarar kwanan nan a Kaduna.

Shugaban kasar ya bada shawara ga Dakarun Sojojin na Najeriya su bi ka’idar ka’ida wajen kokarin kare martabar Najeriya da kuma tsare kan iyakokin kasar daga wata barazana daga waje.

Idan ba ku manta ba, shugaban kasar ya kaddamar da asibitin Sojoji na 44 da ke Garin Kaduna da aka bunkasa a cikin wannan makon. Wannan zai taimaka wajen inganta harkar kiwon lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel