An yi tsit bayan Kotu ta ce masu karbar albashi fiye da guda su dawo da kudi

An yi tsit bayan Kotu ta ce masu karbar albashi fiye da guda su dawo da kudi

Tsofaffin Gwamnoni da Mataimakansa da ke rike da kujerun Ministoci ko majalisar tarayya ba su ce komai game da hukuncin da kotu ta yi kwanan nan a kan karbar albashi biyu ba.

A wata shari’a da Alkalin kotun tarayya da ke zama a Legas ya yi, ya bukaci tsofaffin Gwamnonin Najeriya da yanzu su ke rike da wasu mukamai, su dawo da kudin fanshon da su ka karba.

Bugu da kari Kotu ta nemi gwamnatin Najeriya ta hannun AGF ta kalulabalanci halaccin biyan gwamnonin baya fansho. Ministan shari’a ya bayyana cewa su na duba wannan hukunci.

Ministan ya yi wannan jawabi ne ta bakin Mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai, Dr Umar Jibrilu Gwandu, wanda ya fadawa Daily Trust cewa, za a tsaida matsaya a kan lamarin.

Akwai tsofaffin Gwamnoni fiye da 50 da su ka rika karbar kudi biyu a lokuta daban-daban a kasar. Yanzu haka binciken da Jaridar ta yi ya nuna cewa akwai Sanatoci 16 da ke cin albashi biyu.

KU KARANTA: An bayyana albashi da alawus na 'Yan Majalisar Wakilai

Wadannan Sanatoci da su ka taba yin gwamna su ne: Rochas Okorocha, Ibikunle Amosun, Kashim Shettima, Tanko Al-Makura, Ibrahim Gaidam, Orji Kalu, Theodore Orji da Sam Egwu.

Sauran ‘Yan majalisar sun hada da Danjuma Goje, Chimaroke Nnamani, Ibrahim Shekarau, Kabir Gaya, Adamu Aliero, Aliyu Magatakarda Wamakko, Gabriel Suswam da Abdullahi Adamu.

Akwai mutane biyu da su ka taba rike kujerar mataimakin gwamna a kudancin Najeriya da yanzu su ke majalisar dattawa. Wadannan Sanatoci su ne Biodun Olujimi da Enyinnaya Abaribe.

Kuma akwai tsofaffin Gwamnoni 9 da yanzu su ka zama Ministoci. Har ila yau akwai Mataimakan gwamnoni na-da, da yanzu Ministoci ne a Gwamnatin nan. Duk sun ke cewa uffan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel