Jigo a jam'iyyar APC ya gurfana a kotu saboda 'zagin gwamna' a kafar sada zumunta

Jigo a jam'iyyar APC ya gurfana a kotu saboda 'zagin gwamna' a kafar sada zumunta

Hukumar 'yan sandan jihar Neja na tuhumar wani dan siyasar Najeriya da zargin gwamnan jihar rashawa tare da nuna halin ko in kula ga tituna.

Abubakar Katcha ya gurfana a gaban wata kotun majistare ne a Minna, a ranar Laraba.

An bada belinsa a kan N500,000 bayan da ya kwana tsare wajen 'yan sanda. An kamashi ne sakamakon koken da shugaban ma'aikata, Ibrahim Balarabe ya kai.

A bayanin farko da mai koken ya yi game da Katcha, wanda jaridar Premium Times ta samu, an zargi dan siyasar da hada baki da wani mutumi wajen wallafa wani rubutu a kafar sada zumuntar zamani, wanda zai iya hankulan 'yan jihar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabbin sakatarorin gwamnati 9 (Jerin sunaye)

'Yan sandan sun ce, Katcha ya zargi gwamnan jihar ne da almundahanar waskar da wasu dukiyoyin gwamnati zuwa amfaninsa da na iyalinsa.

"Hakazalika, jihar Neja ta kasa gyara titunan jihar," kamar yadda zargin ya karanto.

'Yan sandan sun ce laifin ya cika karo da sashi na 97 sakin layi na 2, sashin na 397,393 da kuma 114 na dokokin penal code.

Mai shari'a Hauwa Yusuf ta bada belin Katcha tare da dage sauraron shari'ar zuwa 17 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel