Mutuwa riga ce bata fita: Gwamnan jahar Akwa Ibom ya rasa mahaifinsa

Mutuwa riga ce bata fita: Gwamnan jahar Akwa Ibom ya rasa mahaifinsa

Gwamnan jahar Akwa Ibom, Gwamna Udom Emmanuel ya rasa mahaifinsa Gabriel Nkanang ga mutuwa a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani hadimin gwamnan mai suna Aniekeme Finbarr ne ya bayyana mutuwar mahaifin gwamnan a wani rubutu da yayi a manhajar WhatsApp, inda yace mamacin ya mutu yana da shekara 90 a duniya.

KU KARANTA: Kafa sabbin masarautu: Ganduje ya fasa majalisar dokokin jahar Kano gida biyu

Shi ma yayan gwamnan, kuma babban dan mamacin, Gabriel Nkanang ya tabbatar da mutuwar mahafin nasu, inda yace zasu sanar da shirye shiryen bikin binneshi nan bada jimawa ba.

Jahar Akwa Ibom na daya daga cikin jahohin yankin kudu maso kudancin kasar nan dake karkashin mulkin jam’iyyar PDP, kuma ita ce jahar da tafi sauran jahohin yawan rijiyoyin mai da ake hakar danyen man fetur a cikinsu.

Duk dai a yankin kudu maso kudancin Najeriyan, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Bayelsa ta tabbatar da mutuwar wasu miyagun mutane biyu da ake zargi da satar mutane tare da yin garkuwa dasu, ta hanyar banka musu wuta da wasu fusatattun matasa suka yi.

An kama miyagun ne bayan sun yi garkuwa da wasu dalibai guda 3 da suka fito daga kwalejin kiwon lafiya da kimiyya dake Otuogidi, inda jama’a suka kamasu a Otuagala cikin karamar hukumar Ogbia.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana damuwarsa game da yadda gwamnonin jahohi suke rike hakkokin kudaden fanshon tsofaffin gwamnoni.

Lamido yace a matsayinsa na tsohon gwamnan jahar Jigawa, N667,000 kacal ake biyansa a matsayin kudin fansho a duk wata, amma duk da karancin kudin, tsawon shekara daya kenan ko sisi bai gani ba.

Lamido yace kudin da ake biyansa bai kai N700,000 da tsohon gwamnan jahar Kaduna, Balarabe Musa yace ana biyansa ba. “Wanda shi ya yi mulki ne sama da shekaru 30 da suka gabata, don haka nake kira da a bi doka wajen biyanmu hakkokinmu.” Inji shi

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel