Kafa sabbin masarautu: Ganduje ya fasa majalisar dokokin jahar Kano gida biyu

Kafa sabbin masarautu: Ganduje ya fasa majalisar dokokin jahar Kano gida biyu

Bukatar da mai girma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya mika gaban majalisar dokokin jahar ta neman su tattauna tare da amincewa da kudurin dokar kafa sabbin masarautu guda 4 a jahar ta raba kawunan yan majalisar.

Ganduje dai ya sake aika ma majalisar kudurin dokar kafa sabbin masarautun ne bayan wata kotu a Kano ta rusa masarautun sakamakon kura kurai da tace an tafka a yayin da ake samar da dokar kafa masarautun tun da farko, wanda haka ne yasa gwamnan ya sake sabon shiri.

KU KARANTA: Tsohon gwamna Sule Lamido ya bayyana gaskiyar abin da ake biyansa a matsayin fansho

Idan har majalisar ta amince da kudurin dokar har ta tabbatar da shi kamar yadda gwamnan yake muradi, dokar za ta bashi daman kafa masarautu guda 4 masu daraja ta daya wanda zasu yi gogayya da masarautar Kano ta Sarki Muhammadu Sunusi wajen matsayi.

Sai dai rahoton jaridar The Nation ta ruwaito an kasa samun daidaito tsakanin yan majalisun, inda suka kwashe tsawon sa’o’i uku suna tafka muhawara game da kudurin har ma ta kai ga an koma cacar baki, haka kuma aka tashi barambaram ba tare da an cimma wata matsaya ba.

Ganin rai ya baci, hankula sun tashi, yasa kaakakin majalisar ya dage cigaba da tattauna batun zuwa ranar Alhamis, 5 ga watan Disamba.

Duk da cewa zaman sirri majalisar ta yi yayin tattauna kuduri, amma rahotanni sun tabbatar da cewa an hana yayan jam’iyyar PDP dake majalisar tofa albarkacin bakinsu game da dokar, sakamakon duk kokarin da suka yi na neman a basu izinin yin magana ya ci tura.

Kuma da yake yan PDP 12 ne kacal majalisar, hakan na nufin basu da tasirin kawo ma dokar kancal saboda yawansu bai taka kara ya karya ba a idon doka, basu kai adadin biyu bisa uku da nema wajen samun rinjaye ba, don haka idan har kan yayan jam’iyyar APC ya hadu a kan wannan kuduri, magana ya kare.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel