Babbar magana: Kwanan nan za a fara samun zindikan jahilai a majalisar Najeriya - Rochas Okorocha

Babbar magana: Kwanan nan za a fara samun zindikan jahilai a majalisar Najeriya - Rochas Okorocha

- Tsohon gwamna kuma sanata a halin yanzu mai wakilta jihar Imo ta yamma, ya koka da katutun jahilci da ake fama dashi a kasar nan

- Ya bayyana cewa, akwai yiwuwar watarana a samu dan majalisar tarayyar Najeriya da bai iya rubutu ko karatu ba

- A bayanin mahukuncin, ya ce inama za a kara makarantu da jami’o’i a fadain kasar nan ta yadda za a fatattaki jahilci da wuri

Tsohon Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a fara samun wadanda basu iya karatu ba a matsayin ‘yan majalisar tarayyar kasar nan.

A wani bidiyo da ya bazu cikin kwanakin nan, Rochas Okorocha wanda ya wakilci jihar Imo ta yamma a majalisar dattijai, yace akwai bukatar a dau mataki don hana wadanda basu iya karatu ba zama ‘yan majalisar tarayya a Najeriya.

“Dole ne ‘yan Najeriya su san cewa, iya karatu da rubutu a arewacin Najeriya na da illa ga kowanne yanki na kasar nan. Maganar ilimi kuwa ta shafemu dukkanmu. Na so akwai dokar da zata ce wa kowa, ‘saurara, bamu da isassun makarantu da kuma jami’o’i a Najeriya. Mu kirkiro wasu masu matukar yawa da zasu taimaka wajen rage rashin karatu a kasar nan."

KU KARANTA: Babbar magana: Sayar da wiwi a jinina ne, dan haka babu wanda ya isa ya hanani - Wani dilan wiwi ya fadawa hukumar NDLEA

“Damuwata itace, idan ba mu gaggauta yin wani abu da wuri ba, wannan rashin ilimin zai iya katutu a arewa. Watarana kuwa, zamu iya samun wakilan tarayya daga arewacin kasar nan da ba zasu iya magana da turanci ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel