Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabbin sakatarorin gwamnati 9 (Jerin sunaye)

Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabbin sakatarorin gwamnati 9 (Jerin sunaye)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada sakatarorin dindindin na gwamnatin tarayya.

Mukaddashin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ta bayyana hakan a ranar Laraba.

Ta bayyanhakan ne a takardar da Mrs. Olawunmi Ogunmosunle, daraktar yada labarai ta ofishin shugaban ma’aikatan tarayya ta sa hannu.

Kamar yadda ta sanar, jerin sunayen manyan sakatarorin gwamnatin, jihohinsu da yankunansu sune:

1. Injiniya Musa Hassan, jihar Barno.

2. Ahmedd Aliyu, jihar Neja.

3. Mrs. Olushola Idowu, jihar Ogun.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da belin 'Mama Boko Haram' kan N30m

Mutane shida da aka zaba saboda yankinsu da aka bi sun hada da:

4.Andrew David Adejoh, yankin Arewa ta tsakiya

5. Umar Idris Tijjani, Arewa maso gabas

6. Dr. Nasir Sani Gwarzo, Arewa maso yamma

7. Injiniya Nebeolisa Victo Anako, Kudu maso gabas

8. Fashedemi Temitope Peter, Kudu maso yamma

9. Dr. (Mrs) Evelyn Ngige, Kudu maso kudu.

“Za a sanar da ranar rantsar dasu tare da ma’aikatunsu nan ba da dadewa ba,” in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel