Tsohon gwamna Sule Lamido ya bayyana gaskiyar abin da ake biyansa a matsayin fansho

Tsohon gwamna Sule Lamido ya bayyana gaskiyar abin da ake biyansa a matsayin fansho

Tsohon gwamnan jahar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana damuwarsa game da yadda gwamnonin jahohi suke rike hakkokin kudaden fanshon tsofaffin gwamnoni, inda yace kamata ya yi su yi biyayya ga dokokin da suka amince a biya tsofaffin gwamnoni hakkokinsu.

Lamido ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da BBC Hausa, inda yace a matsayinsa na tsohon gwamnan jahar Jigawa, N667,000 kacal ake biyansa a matsayin kudin fansho a duk wata, amma duk da karancin kudin, tsawon shekara daya kenan ko sisi bai gani ba.

KU KARANTA: Jama’a sun cafke masu garkuwa da mutane, sun banka musu wuta har lahira

Lamido yace kudin da ake biyansa bai kai N700,000 da tsohon gwamnan jahar Kaduna, Balarabe Musa yave ana biyansa ba. “Wanda shi ya yi mulki ne sama da shekaru 30 da suka gabata, don haka nake kira da a bi doka wajen biyanmu hakkokinmu.

“A lokacin da nake gwamna akwai wata kwamiti da aka kafa domin daidaita albashin ma’aikata da na alkalai, mun tattauna dasu, kuma aka tsara abin da ya kamata a biya, ni da kaina na rattafa hannu kan dokar, amma ba zan iya tuna takamaimen kudin ba.

“Amma dai na san daga cikin wadanda zasu amfana akwai tsofaffin gwamnoni, mataimakansu, tsofaffin kaakakin majalisa, mataimakansu. A matsayina na tsohon gwamna ina da hakkin a bani gidan, motoci, da kuma a kaini asibiti a kasar waje don duba lafiyata, amma ko daya ba’a min ba, illa N667k da ake biyana, shi ma an dakatar. Haka zalika Saminu Turaki ba’a biyansa, shi ma Ali Sa’adu haka.” Inji shi.

Sai dai Lamido ya gargadi gwamnan jahar Jigawa, Muhammad Badaru da cewa idan har yana kallonsu a matsayin yan adawa ne, toh lokaci zai yi da shi ma zai shiga sahunsu na tsofaffin gwamnoni.

Bugu da kari Lamido ya bayyana damuwarsa game da yawan kudin fanshon tsohon gwamna a jahar Zamfara, inda yace naira miliyan 10 ya yi yawa, inda yace idan jahohi masu arziki kamar Legas, Ribas da Akwa Ibom zasu iya biyan miliyan 10, mai zai kai jahar Zamfara biyan wannan kudi?

Daga karshe Lamido yace su ma tsofaffin shuwagabannin kasa, tsofaffin shuwagabannin hafsoshin soja, tsofaffin shuwagabannin kwastam, tsofaffin shuwagabannin hukumar kurkuku, tsofaffin shuwagabannin hukumar shige da fice, tsofaffin Alkalan Alkalai da tsofaffin Alkalan kotun koli duk suna more irin wannan makudan kudade.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel