Bayan kimanin shekaru 20, WAEC ta kwace sakamakon jarrabawar mutum 10 (Jerin sunaye)

Bayan kimanin shekaru 20, WAEC ta kwace sakamakon jarrabawar mutum 10 (Jerin sunaye)

- WAEC ta fitar da sunayen wasu da suka rubuta jarrabawa da aka samu da laifin magudin jarrabawa tsakanin shekarar 1992 zuwa 2014

- Hukumar ta WAEC ta kwace sakamakon jarrabawar da ta bawa mutane 10 da abin ya shafa

- Kazalika, hukumar JAMB ta ce tana aiki tare da Hukumar samar da katin zama dan kasa (NIMC) don gano wadanda ke rubuta jarrabawarta

Bayan bincike da aka gudanar da ya nuna cewa wasu ba sune suka rubutta jarrabawar da suke amfani da ita ba, Hukumar shirye jarrabawar kammala sakandare ta WAEC ta kwace sakamakon jarrabawar wasu dalibai daga shekarar 1992 zuwa 2014.

PM news ta ruwaito cewa hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB) ce ta fitar da sunayen mutanen 10 da abin ya shafa a ranar Litinin 2 ga watan Disamba.

Ga dai sunayensu da lambobin jarrabawarsu kamar haka:

1. Ukaumunna C. December 1992 (NGSP 0233613)

2. Chinna H. December 1993 (NGSP 0572427)

3. Koffi E. December 1993 (NGSP 0455669)

4. Oham J. December 1994 (NGSP 0177271)

5. Mbara G. December 2001 (WNR 2248072)

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da belin 'Mama Boko Haram' kan N30m

6. Ifo S. December 2001 (NGWASSCP 1307367)

7. Ugwu P. December 2005 (NGWASSCP 4534182)

8. Anene J. December 2008 (NGWASSCP 5505913)

9. Ogbenna C. December 2011 (NGWASSCP 06927486)

10. Nwangwu I. December 2014 (NGWASSCP 8392056)

A yunkurinta na rage magudin jarabawa, hukumar JAMB ta ce tana aiki tare da Hukumar samar da katin zama dan kasa (NIMC) don tabbatar da sunaye da lambobin wadanda za su rubuta jarrabawa yayin jarrabawan da kuma bayan an gama.

Hukumar ta ce, "Domin yin rajistan UTME na 2020 cikin sauki, mun tsara yadda za mu gwada sabon tsari na tantance wadanda za suyi JAMB ta hanyar amfanin da lambar dan kasa NIN."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel