'Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun sace hakimi da wasu mutum 6 a Neja

'Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun sace hakimi da wasu mutum 6 a Neja

Wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne a ranar Talata da asubahin Laraba sun kai hari a wasu garuruwa a karamar hukumar Neja inda suka kashe a kalla mutane takwas.

Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun kuma sace hakimin garin Madaki, Alhaji Zakarai Ya'u, matarsa da dagacin garin Kukoki da wasu mutane hudu kamar yadda wasu mazauna kauyen da suka tsere suka bayyana.

Daya daga cikinsu ya ce, "Sun kuma yi awon gaba da sakataren karamar hukumar da wani tsohon soja da ya yi murabus."

Ya ce sun kuma sace wata mace mai shayarwa tare da jaririn ta.

Wasu mazauna garin da ba su son a bayyana sunansu 'saboda akwai yiwuwar za su dawo' sunyi bayyanin cewa 'yan bindigan fiye da 100 sun isa garin misalin karfe 10 na daren Talata kuma suka fara harbe-harbe kafin suka fara bi gida-gida suna fashi.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da belin 'Mama Boko Haram' kan N30m

Ya ce maharan sun harbe mutane bakwai yayin da suka ja mutum daya da karfi da yaji suka yi masa yankan rago.

Ya kara da cewa biyar cikin mutanen da aka yi wa rauni da bindiga suna asibitin Kagara inda ake kulawa da su.

An ruwaito cewa sun yi wa gidajen al'umma da shaguna fashi inda suka kwashe kayayyakin abinci har ma da shanu da wasu dabobbin.

A garin Madauka, duk da cewa ba a tabbatar da rasa rai ba, an ce 'yan bindigan sun yi wa mutane fashi, sun kuma sace shanu yayin da wasu mutane kuma an neme su an rasa.

Gwamnatin jihar ta ce tana hadin gwiwa da jami'an tsaro domin magance fitinar.

Sanarwar da gwamna Sani Bello ya fitar da bakin sakataren watsa labarai, Misis Mary Noel berje ya ce jami'an tsaro tuni sun fara bincika garin da niyyar gano 'yan bindigan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel