Fitattun 'yan siyasa 5 da suka ci zabe a 2019 amma kuma yanzu sun rasa kujerunsu

Fitattun 'yan siyasa 5 da suka ci zabe a 2019 amma kuma yanzu sun rasa kujerunsu

Wasu sanannun 'yan siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da cewa sun samu nasarar lashe zabe a kujeru daban - daban daga sassan kasa a zaben 2019 sun rasa kujerunsu sakamakon hukuncin kotu.

Wasu daga cikin irin wadannan 'yan siyasa sun rasa kujerunsu ne sakamakon kwace nasararsu da kotu ta yi ko kuma sun fadi zabe bayan kotu ta bayar umarnin sake gudanar da zaben kujerar da aka bayyana sun samu nasarar lashe wa da farko.

Fitattu daga cikin 'yan siyasa da wannan lamari ya shafa akwai;

1. Senator Adedayo Adeyeye

Kotu ce ta yanke hukunci tsige kakakin majalisar dattijai, Adedayo Adeyeye, daga kujerar wakilicin jihar Ekiti ta kudu a majalisar dattijai.

Adeyeye, tsohon kakakin jam'iyyar PDP, mamba ne yanzu haka a jam'iyyar APC mai mulki.

Kotun daukaka kara ta bayyana Sanata Biodun Olujimi na jam'iyyar PDP a matsayin halastaccen wanda ya lashe kujerar wakilcin Ekiti ta kudu a majalisar dattijai.

Olujimi, daya daga cikin shugabannin majalisar dattijai, tsohouwar mataimakiyar gwamna ce a jihar Ekiti. Tun a kotun sauraron korafin zabe ta fara samun nasara kafin daga bisani kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun farko ta yanke.

2. Abdulmumin Jibrin

Abdulmumin Jibrin, mamba ne a majalisar wakilai daga mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano, kuma a ranar 1 ga watan Nuwamba me kotun daukaka kara ta soke zabensa tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a cikin kwanaki 90.

Dan takarar jam'iyyar PDP, Aliyu Datti Yako, ne yake kalubalantar nasarar da Abdulmumin Kofa ya samu a zaben 2019.

3. Ned Nwoko

Tun da farko kotu ce ta kwace takarar kujerar sanatan jihar Delta ta arewa daga hannun Sanata Peter Nwaoboshi ta bawa attajirin dan kasuwa Ned Nwoko, duk a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Sai dai a cikin watan Afrilu wata kotun tarayya da ke Abuja ta warware hukuncin kotun farko, inda ta bayyana cewa Nwaoboshi ne halastaccen dan takarar jam'iyyar PDP, ba Nwoko ba, kamar yadda kotun farko ta yanke hukunci.

DUBA WANNAN: Ba lallai PDP ta shiga zabukan da za a gudanar nan gaba ba - Secondus

Duk da Nwoko ya daukaka kara zuwa kotun koli har sau biyu, kotun ta yi watsi da kararsa bisa dalilin cewa bata da tushe.

4. Alhaji Bala Hassan

Kotun daukaka kara ce ta cire Alhaji Bala Hassan daga kujerar wakilcin Sokoto ta Kudu da Sokoto ta arewa a majalisar wakilai.

Dan takarar jam'iyyar PDP, Abubakar Abdullahi, shine ya shigar da karar kalubalantar nasarar da Hassan ya samu. Kotu ta bayar da umarnin a sake gudanar da zabe a cikin kwanaki 90.

5. Dino Melaye

A ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba, aka kammala zaben kujerar sanatan jihar Kogi ta yamma, inda dan takarar jam'iyyar APC, Smart Adeyemi, ya samu nasarar kayar da Sanata Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP.

Kotu ce ta soke zaben Dino Melaye tare da bawa hukumar INEC umarnin sake gudanar da sabin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel