Jama’a sun cafke masu garkuwa da mutane, sun banka musu wuta har lahira

Jama’a sun cafke masu garkuwa da mutane, sun banka musu wuta har lahira

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Bayelsa ta tabbatar da mutuwar wasu miyagun mutane biyu da ake zargi da satar mutane tare da yin garkuwa dasu, ta hanyar banka musu wuta da wasu fusatattun matasa suka yi.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito an kama miyagun ne bayan sun yi garkuwa da wasu dalibai guda 3 da suka fito daga kwalejin kiwon lafiya da kimiyya dake Otuogidi, inda jama’a suka kamasu a Otuagala cikin karamar hukumar Ogbia.

KU KARANTA: Buhari ya kaddamar da sabon tsarin gudanarwar tsaro na gwamnatinsa

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Asinim Butswat ya bayyana cewa a ranar Talata, 3 ga watan Disamba aka kama masu garkuwan, amma jim kadan bayan Yansanda sun kamasu ne sai matasan yankin suka kwacesu daga hannunsu, nan take suka banka musu wuta.

“Bayan samun bayanan sirri a ranar 3 ga watan Disamba da misalin karfe 4:25 na yamma wata rundunar hadaka data kunshi Yansanda da yan banga suka kutsa kai cikin dajin Otuagala na karamar hukumar Ogbia inda suka ceto daliban su uku da miyagun suka sacesu a ranar 2 ga watan Disamba.

“A yanzu haka daliban suna cikin koshin lafiya, sai dai masu garkuwan guda biyu da Yansanda suka kama sun bakunci lahira bayan jama’a sun kwacesu daga hannun Yansanda sun banka musu wuta, sa’annan Yansanda sun kwato wasu katako guda biyu da suka yi ma siffar bindigar AK-47.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata sabuwar tsarin gudanar da tsaro a Najeriya da gwamnatinsa ta kirkira, mai taken “Dawo da tsaro a Najeriya”.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da sabon tsare tsaren ne a wani taro daya gudana a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, jim kadan kafin fara taron majalisar zartarwa.

Manufar wannan sabuwar tsari shi ne don shawo kan babbar kalubalen matsalar tsari da ta dabaibaye najeriya, a jawabinsa, shugaba Buhari yace an samar da tsare tsaren ne bayan tattaunawa tare da tuntuba tsakanin dukkanin hukumomin tsaron Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel