Yabon gwani ya zama dole: Jami’ar Najeriya za ta karrama shugaban kasar Rwanda

Yabon gwani ya zama dole: Jami’ar Najeriya za ta karrama shugaban kasar Rwanda

Jami’ar gwamnatin tarayya ta tunawa da marigayi Obafemi Awolowo dake garin Ile-Ife jahar Osun, OAU, za ta karrama shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame tare da wasu zakakuran yan Najeriya guda uku a bikin yaye dalibanta karo na 44.

Mai magana da yawun jami’ar, Abiodun Olarewaju ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, 4 ga watan Disamba, inda yace daga cikin wadanda jami’ar za ta karrama akwai Biodun Shobanjo, babban dan kasuwa daya shahara wajen sadarwar zamani.

KU KARANTA: Buhari ya kaddamar da sabon tsarin gudanarwar tsaro na gwamnatinsa

Sauran sun hada da shugaban bankin shiga da fitar da kayayyaki na Afirka, AFREXIMBANK, Benedict Oramah da kuma babban darakta kuma shugaban bankin First Bank Nigeria Ltd, Uwargida IbukunOluwa Awosika.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito sanarwar ta bayyana cewa jami’ar za ta karrama shugaba Kagame ne sakamakon shugabanci nagari da yake gudanarwa a kasar Rwanda, musamman rawar daya taka wajen kawo karshen kisan kare dangi da aka yi a kasar.

Haka zalika jami’ar OAU za ta karrama Shobanjo ne duba da tsawon shekarun daya kwashe yana taka muhimmiyar rawa a fannin sadarwa a Najeriya, tsawon shekaeu 50 kenan, sai kuma lambar karramawa ga Ben Oramah a dalilin tarin nasarorin daya samu a bangaren karatu da neman ilimi.

Daga karshe, jami’ar za ta karrama Awosika sakamakon gudunmuwar da ta bayar wajen cigaban kananan masana’antu a Najeriya da kuma tallafin a take baiwa marasa karfi.

Za’a gudanar da bikin yaye daliban jami’ar OAU tare da karrama wadannan manyan mutane ne a tsakanin ranakun 11 da 14 ga watan Disamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel