Buhari ya kaddamar da sabon tsarin gudanarwar tsaro na gwamnatinsa

Buhari ya kaddamar da sabon tsarin gudanarwar tsaro na gwamnatinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata sabuwar tsarin gudanar da tsaro a Najeriya da gwamnatinsa ta kirkira, mai taken “Dawo da tsaro a Najeriya”.

Legit.ng ta ruwaito shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da sabon tsare tsaren ne a wani taro daya gudana a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, jim kadan kafin fara taron majalisar zartarwa.

KU KARANTA: Jerin sunayen kwamishinoni 19 da gwamnan Zamfara ya aika ma majalisar dokokin jahar

Buhari ya kaddamar da sabon tsarin gudanarwar tsaro na gwamnatinsa

Buhari ya kaddamar da sabon tsarin gudanarwar tsaro na gwamnatinsa
Source: Facebook

Manufar wannan sabuwar tsari shi ne don shawo kan babbar kalubalen matsalar tsari da ta dabaibaye najeriya, a jawabinsa, shugaba Buhari yace an samar da tsare tsaren ne bayan tattaunawa tare da tuntuba tsakanin dukkanin hukumomin tsaron Najeriya.

Sabon tsarin gudanar da tsaron ya bayar da fifiko ga tsaron rayukan jama’a, kirkirar sabbin dabarun magance matsalolin tsaro, sabbin dabarun kare rayukan jama’a da kuma dabarun mayar da martani ga matsalolin tsaro cikin gaggawa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Gida Mustapha, babban mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro, Babagana Munguno.

Sauran sun hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo Agege, kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ministan tsaro, Aminu Magashi da ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola.

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Sheikh Zikrullah Olakunle Hassan a matsayin sabon shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai ta Najeriya biyo bayan karewar wa’adin mulkin tsohon shugaban hukumar, Abdullahi Mukhtar.

Buhari ya sanar da nadin Zikrullah ne cikin wata wasika dake dauke da sunan Zikrullah da sauran sabbin kwamishinonin hukumar daya aika ma majalisar dattawan Najeriya domin ta tantancesu, kamar yadda majalisar ta tabbatar a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Twitter.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel