Kwamitin Majalisa ya koka bayan an ba HLSI kwangilar tsaron ruwan Najeriya

Kwamitin Majalisa ya koka bayan an ba HLSI kwangilar tsaron ruwan Najeriya

Kwamitin hadaka mai kula da harkar kudi da ruwa da kuma Sojojin ruwa na majalisar wakilai da dattawa bai gamsu da aikin kula da hanyoyin ruwan Najeriya da aka ba wani kamfanin Israila ba.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto a Ranar 4 ga Watan Disamban 2019, wannan kwamiti na majalisar tarayya ba ya goyon bayan ace kamfanin kasar wajen ne ya ke kula da ruwan kasar.

Bugu da kari kwamitin majalisun ya nuna dar-dar game da labarin da ya ji na cewa wani jirgi dauke da makamai da harsashi da Dakarun sojojin ruwa daga Israila su na tafe zuwa Najeriya.

Wadannan Jami’an Soji na kasar ta Israila za su zo Najeriya ne da nufin samar da tsaro a kan hanyoyin ruwan kasar. ‘Yan majalisar sun yi wannan jawabi ne wajen wani bincike da su ke yi.

Majalisar ta na binciken dakatar da kwangilar tsaro na makudan kudi da aka yi. A baya an ba wani kamfanin gida mai suna OMS aikin tsare ruwan kasar, daga baya aka karbe aka ba HLSI.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bar Daura; ya wuce Garin Kaduna

An fara maganar kashe kwangilar ne a lokacin da Sanatan Ribas, George Sekibo ya tasa shugaban Sojin ruwan kasar nan a gaba game da batun aikin da Israila su ke yi a kan ruwan Najeriya.

Sekibo ya ke tambaya: “Ka na da labarin cewa hukumar NIMASA ta bada wata kwangila mai suna Deep Blue Sea ta fam Dala miliyan 195.3 ga wani Kamfanin kasar Israila mai suna HLSI.”

Sanatan ya dada da cewa kamfanin HLSI zai rika kare ruwan Najeriya. Shugaban hafsun Sojin Najeriya, ya amsawa Sanatan da cewa ya san da labarin wannan aiki da duk yadda ake ciki.

Sanatocin sun yi tir da yadda aka karbe aikin lura da ruwan kasar daga kamfanin gida na OMSL, aka ba kamfanin kasar waje. Admiral D. Tarioworio ne ya wakilci babban jami’in Sojan a zaman.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel