Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da belin 'Mama Boko Haram' kan N30m

Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da belin 'Mama Boko Haram' kan N30m

Wata babban kotun jiha da ke zamanta a Maiduguri a ranar Laraba ta bayar da belin Barrista Aisha Alkali Wakili da aka fi sani da Mama Boko Haram da wasu mutane uku kan tuhumar da ake musu na damfarar kudi har naira miliyan 62.

Mai shari'a Aisha Kumalia ta bayar da belin Wakil a kan kudi naira miliyan 30 tare da mutane biyu da za su tsaya mata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Alkalin ta yi gargadin cewa muddin wadanda ake zargin suka ki gurfana a kotu yayin shari'ar za ta janye belin da ta ba su.

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da wadanda ake zargin kan zarginsu da laifuka da suka hada da cuta, rashin gaskiya da niyyar damfara.

DUBA WANNAN: 'Yar Buhari ta kammala digiri da sakamako mafi daraja daga jami'ar UK

Wadanda ake zargin sun hada da shugaban gidauniyar Complete Care and Aid Foundation, CCAF, Barrista Aisha Wakil; Manajan CCAF, Prince Lawal Shoyede; Manajan shirin, Tahiru Saidu Daura da Kassim Musa Maiduguri.

Ku cigaba da bibiyar mu don samun cikakken rahoton...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel