Mashahuran attajirai 10 da ke harin kujerar gwamnan APC da za a yi zabe a 2021

Mashahuran attajirai 10 da ke harin kujerar gwamnan APC da za a yi zabe a 2021

Wani rahoto da jaridar The Guardian ta fita yayi ikirarin cewa a kalla mashahuran masu hannu da shuni 10 ne ke shirin neman kujerra gwamnan jihar Anambra a shekarar 2021.

Kamar yadda rahoton ya nuna, sanannu a cikinsu sune wadanda suka nemi kujerar a 2013, sun hada da: Andy Uba, Tony Nwoye, ifeanyi Ubah da Godwin Ezeemo.

Sauran wadanda suka bayyana alamun harin kujerar sun hada da: Chief Osita Chidoka, Professor Chukwuma Soludo, Senator Uche Ekwunife, George Moghalu, Chief Stanley Uzochukwu da Chief Nicholas Ukachukwu.

Uba, Nwoye da Moghalu duk ‘yan jam’iyyar APC ne inda Uzochukwu, Ukachukwu da Soludo duk ‘yan jam’iyyyar APGA ne.

Chidoka da Ekwunife kuwa ‘yan jam’iyyar PDP ne, Ubah dan jam’iyyar YPP sai kuma Ezeemo dan jam’iyyar PPA ne.

A halin yanzu, maganar yanki da ubangida ce suke samun wajen zama a zancen harar kujerar. Akwai kuma wasu nagartattun halaye na Gwamna Willie Obiano da ake bukatar magajin kujerar ya mallaka.

DUBA WANNAN: Amfanin tafiye-tafiyen shugaba Buhari ga 'yan Najeriya - Hadiminsa

Gwamnan ya bude ido ne tare da lalube kamar yadda aka nuna, don samun wanda zai gajeshi ya dasa daga inda zai tsaya.

Amma kuma jam’iyyar PDP ta musanta ikirarin da aka yi na cewa ta fara gangamin kamfen don nemawa Soludo kujerar

Daya daga cikin ‘yan kwamitin mutane 46 ya nuna damuwarsa ta yadda ake zargin gwamnan da kokarin nada wanda zai gajeshi.

A wani rahoton da kafafen yada labarai suka bayyana a kwanakin nan, ya nuna cewa neman magajin Gwamna Obiano ya fara ne tun kafin zuwan zaben 2021.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel