Sabon albashi: Za mu saka kafar wando daya da gwamnonin jihohi - NLC, TUC

Sabon albashi: Za mu saka kafar wando daya da gwamnonin jihohi - NLC, TUC

- Kungiyar kwadago ta kasa, ta bukaci gwamnatin tarayya da dukkan jihohi da su tabbatar da sabon mafi karancin albashi

- Shugaban kungiyar ta bakin mataimakinsa, ya ce zasu saka kafar wando daya da duk gwamnan da ya ki biya

- Ya tabbatar da cewa, hukumar ta kirkiro da hanyoyi da zata zakulo duk wani gwamnan da ya ki biyan sabon alabshin

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da duk wadanda abun ya shafa da su hanzarta tabbatar da mafi karancin albashin na N30,000.

Shugaban kungiyar kwadagon, Kwamared Ayuba Wabba, wanda Amaechi Asuguni ya wakilta a wani taro da aka yi a Abuja a jiya ne ya sanr da hakan.

Ya kara da bayyana cewa NLC da TUC sun hada hanyoyin gano gwamnonin da suka ki biyan karancin albashin.

“NLC da TUC na bibiyar lamurran kowacce jiha don tabbatar da kowanne gwamna ya biya sabon mafi karancin albashin,” ya ce.

DUBA WANNAN: Kotu ta bukaci sanatoci da su dawo da kudin fansho da suka karba a matsayin tsoffin gwamnoni

Idan zamu tuna, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan sabon albashin ne a watan Afirilu na wannan shekarar 2019.

Tuni dai wasu gwamnonin jihohi suka fara biyan sabon albashin, inda wasu kuma suka yi alkawarin fara biya nan ba da dadewa ba. Amma kuma akwai gwamnonin da suka yi biris da maganar ba tare da sun tofa albarkacin bakinsu ba.

Hakan ne kuwa yasa kungiyar kwadagon ta bayyana cewa, zata sa kafar wando daya da duk gwamnan da ya kalmashe hannu ya ki biyan sabon albashin, kamar yadda dokar kasar nan ta tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
NLC
Online view pixel