Asiri ya tonu: Wani na hannun daman Jonathan na barazanar kashe wani mutumi

Asiri ya tonu: Wani na hannun daman Jonathan na barazanar kashe wani mutumi

- Wani dan Najeriya ya yi bayanin yadda sojojin tawagar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan suka yi barazanar kasheshi

- Mutumin ya bayyana yadda suka mishi barna a mota a kan hanyar zuwa jami’ar Igbinedion inda aka karrama Jonathan

- Ya yi kira ga tsohon shugaban kasar wanda jakadan zaman lafiya ne, da bai dace hadimanshi suna cutar mutane kuma su hanasu kuka ba

Wani dan Najeriya ya je shafinshi na Instagram inda ya wallafa yadda wani hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi barazanar halakashi har lahira.

Kamar yadda ya sanar, yana kan hanyarshi ta zuwa jami’ar Igbinedion ne a kan don halartar bikin yaye dalibai, amma sai suka samu hatsari a kan titin Sapele.

A bayanin da yayi, sojan da yake tsaron tsohon shugaban kasan ya yi barazanar kashe shi saboda an la’anta mishi motarshi da tawagar tsohon shugaban kasar tayi.

A kalaman mutumin: “Da farko dai ina taya Goodluck Jonathan murna a kan karrama shi da aka yi. Kuma ina so jama’a su shaida abunda ya faru dani a titin Sapele, yayin da tawagar tsohon shugaban kasar ke tahowa daga Bayelsa a ranar 29 ga watan Nuwamba 2019.

“Ina kan hanyata daga Delta lokacin da na ci karo dasu. Titin bashi da kyau, shiyasa nayi yunkurin komawa dayan gefen. Babbar mota ce ta tosheni na kasa komawa inda ya kamata. Kawai kuma sai ga tawagar ta iso."

KU KARANTA: Tirkashi: An kama mai hakar kabari a makabarta da yake sayar da kokon kan mutane akan naira 6,000

“Wata mota kirar bas mai lamba NEM 503 AA wacce ke bayan jif mai lamba BR 120 GWA ce ta yi karo da motata kuma ta yi min barna. Na yi wa direban magana a kan barnar da aka yi min, amma sai ya yi barazanar harbeni matukar ban bar wajen ba.”

Ya bayyana yadda ya dinga binsu har Edo. Sun samu matsalar taya. Tuni yayi yunkurin sanar dasu abinda ya faru, amma sai sojoji suka fitar da bindigogi tare da barazanar harbinshi. Sun cigaba da tafiya, inda ya bi su a baya amma sai suka isa jami’ar Igbinedion tare. A nan ne za a karrama tsohon shugaban kasa.

Ya tura takarda ga Chief Dr Mrs Nkechi Mbah don ta san abinda ya faru, amma takardar ta kai mata, bata dau wani mataki ba.

“A matsayin tsohon shugaban kasar na jakadan zaman lafiya, bai dace yana aiki da mutane irinsu ba, wadanda ke tsawwalaa tare da cutar talaka. A don haka ne na yanke hukuncin bayyanawa duniya halin da ake ciki.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel