Assha: Dan sanda ya bindige abokan aikinsa 5 har lahira

Assha: Dan sanda ya bindige abokan aikinsa 5 har lahira

Wani dan sanda cikin dakarun da ke tsaron iyakokin kasar India ya bude wa abokan aikinsa 5 wuta ya kashe su sannan ya harbe kansa kamar yadda 'yan sandan suka ruwaito.

Channels Television ta ruwaito cewa dan sandan mai suna Musudul Rehman da ke aiki rundunar kula da iyakar India da Tibet (IPBP) ya harbe abokon aikinsa a Chhattisgarh, wata jiha da 'yan ta'adda suka lalata.

"Daga bisani ya kuma harbe kansa bayan ya harbi jami'an yan sanda bakwai," a cewar sanarwar da ITBP ta fitar. 'Yan sanda biyu cikin wanda ya harbe sun tsira da raunuka kuma an garzaya da su zuwa Raipur.

DUBA WANNAN: 'Yar Buhari ta kammala digiri da sakamako mafi daraja daga jami'ar UK

Jihar ta Chhattisgarh mai albarkatun kasa tana daya daga cikin jihohi masu fama da talauci a Indiya ind a 'yan tayar da kayan baya na Maosit suka shafe shekaru masu yawa suna fada kan filaye da albarkatun kasa.

An kashe dubban sojoji, 'yan sanda, masu tayar da kayan baya da sauran mutane tun 1960s. Gwamnati ta aiki da dubban 'yan sanda da dakarun sojoji na musamman domin kawar da kungiyoyin masu tayar da kayan bayan.

An samu kunan bakin wake fiye da 300 a sojojin kasar ta Indiya da kuma abinda ake kira 'kisar 'yan uwa' tun 2016 wadda hakan ya saka gwamnati ta dauki matakan rage afkuwar hakan da suka hada da motsa jiki, wayar sauraron koke da sauransu.

A wani rahoton kuma, rundunar sojan kasar ta ce sojoji hudu sun mutu a Kashmir a ranar Talata, uku cikinsu sun fada cikin kankara yayin da dayan shima iska mai dauke da kankara ta kashe shi.

Wasu biyu sun mutu a ranar Asabar bayan fadawa wani ramin kankara mai zurfin mita 4,500 a yankin kankara ta Siachen da ake fada kansa da Pakistan wurin da ya yi kaurin suna a matsayin inda aka fi girke sojoji a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel