Damfarar N70m: EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban jami'ar Najeriya

Damfarar N70m: EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban jami'ar Najeriya

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta damke tsohon shugaban jami;a, Farfesa Emmanuel Kucha a kan zarginsa da a ke da damfarar wasu makuden kudi, a ranar Talata.

Jami’an ofishin hukumar yaki da rashawa na yankin Makurdi ne suka cafke tsohon shugaban jami’ar. Yana fuskantar tuhume-tuhume hudu ne da suka hada da: hadin kai wajen cuta, waddaka da dukiyar gwamnati, amfani da kujerarsa ba ta yadda ya dace ba, da sauransu.

Farfesa Kucha ya musanta zarginsa da ake yi, duk da lauyan masu kara, Y. Tarfa ya sanar da cewa Kucha ya aikata laifin ne a yayin da yake jami’a a tsakanin 2012 zuwa 2017, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Tarfa ya ce, wanda ake zargin ya karba cin hanci ne a yayin da yake aiki a jami’ar. An biya kudin ne zuwa cikin asusun wata sabuwar banki a Najeriya mallakar shugaban jami’ar.

DUBA WANNAN: Abubuwa 10 da yakamata a sani game da sabuwar jami'ar sufuri ta Daura

Tarfa ya bayyana cewa, hakan ya ci karo da tanadin sashi na 18 na dokokin yaki da rashawa da sauran laifuka na 2000.

Lauyan wanda ke kare kanshi, Timothy Dim, ya yi kira ga kotun da ta bada belin wanda yake karewar, sannan a barshi a wajen EFCC din har zuwa lokacin da za a cike sharuddan belin.

Mai shari’a Jastis A. Olajuwon, ya amsa bukatar bada belin amma a naira miliyan goma da kuma tsayyaye daya. Olujuwon ya bayyana cewa, tsayayyen dole ya zamo mai aiki da gwamnatin tarayya ko kuma gwamnatin jihar Benuwe, a mataki na 17.

Hukumar EFCC za ta tsare tsohon shugaban jami’ar har zuwa lokacin da aka cike sharuddan belin. Alkalin ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Janairu na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel