Kotu ta bukaci sanatoci da su dawo da kudin fansho da suka karba a matsayin tsoffin gwamnoni

Kotu ta bukaci sanatoci da su dawo da kudin fansho da suka karba a matsayin tsoffin gwamnoni

- Wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi jihar Legas, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta karbo kudin da tsoffin gwamnoni suka karba lokacin da suke majalisa

- Kungiyar SERAP ta maka gwamnatin tarayya ne a gaban kotun a 2017 akan yadda ta kasa hana gwamnonin karbar kudin fansho har kashi biyu

- Wadanda abun ya shafa sun hada da: Rabiu Kwankwaso, Theodore Orji, Abdullahi Adamu, Sam Egwu, Shaaba Lafiagi, Joshua Dariye, Jonah Jang da sauransu

Wata babban kotun tarayya da ke Ikoyi, jihar Legas, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta karbo kudin fansho da alawus da tsoffin gwamnonin da suke majalisar dattawa suka karba.

Wannan ya fito ne kamar yadda hukumar SERAP ta bayyana a shafinta na tuwita a ranar Laraba. Kungiyar ta maka gwamnatin tarayya ne a gaban kotun a 2017 akan yadda ta kasa hana gwamnonin karbar kudin fansho har kashi biyu.

Ta maka gwamnatin a gaban kuliya ne don kasa samo naira biliyan arba’in din da tsoffin gwamnonin suka karba bayan a lokacin suna sanatoci ko ministoci.

DUBA WANNAN: Amfanin tafiye-tafiyen shugaba Buhari ga 'yan Najeriya - Hadiminsa

Sauran wadanda SERAP ta bayyana da samun wannan garabasar sun hada da Rabiu Kwankwaso, Theodore Orji, Abdullahi Adamu, Sam Egwu, Shaaba Lafiagi, Joshua Dariye, Jonah Jang, Ahmed Sani Yarima, Danjuma Goje, Bukar Abba Ibrahim, Adamu Aliero, George Akume, Biodun Olujimi, Enyinaya Harcourt Abaribe, Rotimi Amaechi, Kayode Fayemi, Chris Ngige da Babatunde Fashola.

Kotun ta ba Abubakar Malami umarnin kalubalantar wannan dokar da ta ba tsoffin gwamnoni, sanatoci ne ko ministoci damar karbar kudin fanshon bayan suna karbar albashi da alawus a wasu ofisoshin siyasa.

Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu 2020, don samun rahoton yarda daga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel