PDP: Jam’iyyun siyasa ba su goyon bayan Shugaban INEC ya yi murabus

PDP: Jam’iyyun siyasa ba su goyon bayan Shugaban INEC ya yi murabus

Kungiyar shugabannin jam’iyyun siyasa 55 a Najeriya sun yi fatali da batun da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ke yi na kiran shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, ya ajiye aiki.

Kamar yadda mu ka samu labari a cikin farkon makon nan, shugaban jam’iyyar NUP, wanda shi ne shugaban wannan kungiya ta jam’iyyun hamayya, Perry Opara ya nuna ba su tare da PDP.

Cif Perry Opara a wani jawabi da ya fitar Ranar Lahadi, ya bayyana cewa ba zai yiwu PDP ta fito ta na kuka a yanzu ba, bayan da ta yi maraba da hukuncin da aka yanke a kan na’urorin zabe.

Opara ya shawarci jam’iyyar adawar da ta nemi ‘Ya ‘yanta da ke Majalisar Tarayya su kawo sauyi a sha’anin zabe a Najeriya a maimakon ta tsaya a gefe ta na yi wa ‘yan kasa wasu koken-karya.

Shugaban kungiyar jam’iyyun ya kuma yi kaca-kaca da PDP a kan kin yi wa dokokin zabe garambawul a lokacin da ta yi shekaru 16 a mulki, inda ya ma nemi jam’iyyar ta ji kunyar kanta.

KU KARANTA: An nada sabon Shugaban NAHCOM bayan karewar wa'adin Mukhtar

“Matsayar kotun koli ita ce tantance masu kada kuri’a shi ne babban shaidar zabe. Don haka ba a aiki da hujjar na’urar da ke tantance masu zabe ta ‘Card Reader’ a gaban kotu.” Inji Cif Opara.

Shugaban jam’iyyar NUP ya ce: “Abin da wannan ya ke nufi shi ne, ko da ace mutum kalilan su ka fito wajen zabe, sai aka samu ‘yan banga sun yi gaba da kayan zaben, su ka dangwale kuri’u…”

Opara ya karasa: “Abin da kurum za su yi shi ne su cike rajistar masu kada kuri’a, sun gama komai.” A da, PDP sun yi murna da wannan hukunci da aka yanke, don haka yanzu su yi shiru.

Wannan ya sa Perry Opara a madadin sauran jam’iyyun hamayyar ya nuna cewa ba su a cikin kiran jam’iyyar PDP na tursasawa Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye aikin da ya ke yi a INEC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel