Abubuwa 10 da yakamata a sani game da sabuwar jami'ar sufuri ta Daura

Abubuwa 10 da yakamata a sani game da sabuwar jami'ar sufuri ta Daura

A ranar Litinin ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya assasa harsashin ginin jami'ar sufuri ta farko a Najeriya. An dora ginin jami'ar ne a mahaifar shugaban kasar da ke Daura a jihar Katsina, arewacin Najeriya.

Ga wasu abubuwa 10 da yakamata mutane su sani game da sabuwar jami'ar sufurin ta farko a Najeriya:

1. A watan Oktoba 2018 ne gwamnatin tarayya ta aminta da fitar da kudin gina jami'ar, kamar yadda hukumar kula da jami'o'i ta Najeriya ta bayyana.

2. Jami'ar zata mayar da hankali ne wajen bincike da bunkasa bangaren sufuri a Najeriya

3. Makarantar mallakin gwamnatin tarayya ce, kuma za a bude wata irinta a jihar Ribas da ke kudancin kasar nan. Ribas jihar Ministan sufuri ce, Chibuike Amaechi.

4. Za a kashe dala miliyan hamsin ne wajen gina jamia'ar, kamar yadda Amaechi ya fada.

5. Kamfanin gine-gine na kasar China mai suna CCECC ne zai gina mashahuriyar jami'ar.

6. Makasudin gina jami'ar kuwa shine cike gibin rashin abin yi a bangaren sufuri, kamar yadda minsitan ya sanar.

DUBA WANNAN: Yadda tsabar kishi ya saka wata mata kashe diyar kishiyarta da guba a Katsina

7. Gwamnatin tarayya na son horar da mutanen da zasu dinga kula da layukan dogo na kasar nan kamar yadda ake wa titunan mota.

8. A halin yanzu, akwai daliban Najeriya da dama dake karantar abinda ya shafi harkar layin dogo a kasar China. Akwai sa ran sune zasu dawo Najeriya don taka rawar gani a matsayin masu bincike a jami'ar ida ta fara aiki.

9. Matasan da gwamnatin Najeriya ta tura kasar China don karantar fannin injiniya na layin dogo ne zasu koyar a makarantar.

10. Ana san ran mashahuriyar jami'ar zata fara karantarwa ne a shekarar 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel