Mu na neman Ifeanyi Ejiofor da Mukarrabansa – Kwamishinan ‘Yan Sanda

Mu na neman Ifeanyi Ejiofor da Mukarrabansa – Kwamishinan ‘Yan Sanda

Jami’an ‘Yan sandan Najeriya na reshen jihar Anambra, sun sa cigiyar fitaccen Lauyann nan Ifeanyi Ejiofor. Jaridar Premium Times ta kawo rahoto a Ranar 3 ga Watan Disamban 2019.

Dakarun su na neman Ifeanyi Ejiofor ne a kan wani rikici da ya barke Ranar Litinin a Garin Oraifite a Anambra. Wannan mummunan rikici ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla hudu.

An ji Kwamishinan ‘Yan sandan Anambra, John Abang, a wani bidiyo da ya fito ta hannun Kakakin ‘Yan sandan a Ranar Talatar nan ya na neman a taimaka masa da labarin Ejiofor.

Kwamishinan ‘Yan sandan ya na cewa: “Jama’a Maza da Mata, ina so in sanar da ‘Yan Najeriya cewa, yanzu haka da na ke magana, Jami’an ‘Yan sanda su na neman Ejiofor da mutanensa.”

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi wa Mayakan Boko Haram lahani

John Abang ya bayyana cewa Barista Ejiofor ya na cikin ‘Ya ‘yan kungiyar IPOB, don haka ake nemansa tare da sauran mutanensa na kungiyar bisa zargin kisan kai, da tuni IPOB ta musanya.

“Ina neman hadin-kan ‘Yan Najeriya daga Arewa, Kudu, Gabas, da Yammacin kasar, da cewa su sanar da ofishin ‘Yan sandan da ke kusa da su, a duk lokacin da su ka ga wannan mutumi.”

Kamar yadda jawabin da Kakakin ‘Yan sandan, DSP Haruna Mohammed, ya fitar ya bayyana, ‘yan sanda za su gurfanar da Ifeanyi Ejiofor tare da Mabiyansa a kotu da zarar an yi ram da su.

Ana zargin ‘Ya ‘yan kungiyar na IPOB mai fafutukar neman kasar Biyafara, da laifin kashe wasu Jami’an ‘yan sanda har biyu. Wannan ya faru ne a Oraifite da ke karamar hukumar Ekwusigo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel