N30, 000 ba zai isa hidimar Ma’aikata ba Inji Godwin Obaseki

N30, 000 ba zai isa hidimar Ma’aikata ba Inji Godwin Obaseki

A Ranar Talata, 3 ga Watan Disamban 2019, Mai girma gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi magana a game da karin albashin Ma’aikata da aka dade ana ta faman ce-ce-ku-ce a kansa.

Mista Godwin Obaseki ya bayyana cewa sabon karin albashin da aka yi, ba zai isa Ma’aikacin gwamnati a wat aba. Gwamnan ya bayyana wannan ne wajen wani taro da NLC ta shirya jiya.

Kungiyar NLC ta ‘Yam kwadagon Najeriya ta gudanar da wani gangami ne a babban birnin tarayya Abuja. Wannan ne karo na 7 da kungiyar Ma’aikatan kasar ta shirya irin wannan taro.

Duk da cewa N25, 000 ne mafi karancin albashi a jihar Edo, gwamnan ya nuna cewa biyan N30, 000 ba zai gagare sa ba. Gwamnan na APC ya ke cewa: “N30, 000 ba zai isa Ma’aikata a wata ba.”

Haka zalika mai girma gwamnan ya kara da cewa ana gina kasa ne da hukumomi masu karfi. Don haka ya ce idan har Najeriya ta na son kai wa ga ci, dole a ba harkar ilmi muhimmanci.

KU KARANTA: 'Dan Majalisa ya bayyana albashi da alawus din da su ke samu

Bayan harkar ilmi, gwamnan ya ce akwai bukatar a maida hankali wajen kiwon lafiya ta hanyar ware kudi da kuma gina wuraren bincike da samar da sauran abubuwan da za su taimaka.

Obaseki ya ke cewa wadannan abubuwa su ne tubulin ginin cigaban duk wata kasa. A cewar gwamnan, Najeriya ba ta bukatar jajirtattun mutane, sai dai jajirtattun hukumomin gwamnati.

“A yayin da mu ke kokarin zama kasar da ta cigaba, abin da ya kamata mu fi maida karfi a kai shi ne abin da mu ka kirkira, dole mu gina abubuwan da zai amfani al’umman da ke zuwa nan gaba.”

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, a na sa jawabin, shugaban kungiyar NASU, Chris Ani, ya koka da halin da Najeriya ta ke ciki. Ani ya ce dogara da man fetur shi ne ya ruguza tattalin kasar nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel