Dalla-dalla: Ɗan majalisar APC ya bayyana kudaden da ya ke karba duk wata

Dalla-dalla: Ɗan majalisar APC ya bayyana kudaden da ya ke karba duk wata

- Wani dan majalisar wakilai yayi bayani dalla-dalla na albashin da yake karba

- Alabi na karbar N700,000 ne a matsayin dan majalisar wakilai

- Sauran alawus din ne jimillarsu ke kai N9m

Akin Alabi dan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazabar Egbeda/Ona-Ara a tarayya. Ya bayyana dalla-dalla na albashinsa a matsayin dan majalisar.

Dan majalisar wakilan wanda dan kasuwa ne, ya yi alkawarin bayanin albashinsa a ranar Juma'a, 5 ga watan Afirilu, in aka fara biyansa albashi.

Bayan watanni kadan da wannan alkawarin, ranar 2 ga watan Disamba sai ya cikashi kuwa.

Duk da dai an dinga caccakarsa a kan tsawon lokacin da ya dauka bai cika alkawarinsa ba, ya cika a sa'o'in farko na ranar Litinin da ta gabata.

DUBA WANNAN: Yadda tsabar kishi ya saka wata mata kashe diyar kishiyarta da guba a Katsina

Kamar yadda Alabi ya ce, yana karbar N700,000 a matsayin albashi. A kuma maganar alawus, yana karbar N3,970,000 da kuma N7,940,000, wanda su kuma yace ana biya ne sau daya a duk shekaru hudu.

A kalamansa: "An sanar dani za a bamu mota a bashi, ta naira miliyan bakwai. Za a bamu kudin kammala aiki har naira miliyan 5 bayan shekaru hudu. Zaka iya kiranshi da kudin sallama ko murabus."

"A takaice dai albashin dan majalisa N700,000 ne. Sauran alawus din ne idan aka hada suke kai N9m. Ba ragi, babu kari." Ya ce.

Ya kara da bayani a kan kudin aiyukan mazabu da ake zargin 'yan majalisar da waskarwa. "Babu dan majalisar da ake ba kudin aiyukan mazabu. Kana zabar aiyukan ne, sai a mika kudin zuwa ga cibiyoyin da aikin ya shafa su aiwatar. Idan kazo majalisar ne don ynkudi, to zata yuwu kana yaudarar kanka ne ko kuma akwai wani abu haramtacce da kake son yi," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel