Mutane 6 kacal su ka shiga jirgin kasan Legas zuwa Ibadan a makon nan

Mutane 6 kacal su ka shiga jirgin kasan Legas zuwa Ibadan a makon nan

Sa’o’i bayan gwamnatin tarayya ta bada sanarwar cewa za a hau jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan ba tare da an biya ko sisi ba, labari ya zo mana cewa jama’a sun kauracewa wannan jirgi.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, daga lokacin da gwamnati ta bada sanarwar hawa jirgin kasar kyauta zuwa yanzu, mutane shida ne kadan su ka yi amfani da jirgin.

A cikin sawu biyu da jirgin ya yi, mutane shida kurum aka samu sun shiga. Layin dogon jirgin mai tsawon kilomita 157, ya fara ne tun daga Garin Iju da ke Legas zuwa Garin Ibadan a jihar Oyo.

Idan ba ku manta ba, a Ranar Asabar, 30 ga Watan Nuwamban 2019, Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya kaddamar da shirin amfani da jirgin kasan bayan an kammala gwajin farko.

Ko da dai ba a kammala aikin dogon ba, an fara amfani da yankin Iju zuwa Ibadan inda tuni aka karkare kwangilar ta wannan bangare. Duk da haka jirgin ya na fama da karancin masu shiga.

KU KARANTA: Buhari ya nada sabon Shugaban hukumar Alhazan Najeriya

Shugaban hukumar NRC ta jiragen kasan Najeriya, Fidet Okhiria, ya bayyana cewa a duk Ranar Allah za a kawo lafiyayyun jirage biyu, wadanda za su dauki mutane 60 zuwa 80 da aka samu.

Hukumar ta yi wa jama’a kashedi cewa jirgin zai dauki wanda su ka yi samamko ne, hakan na nufin wanda ya tafi tashar a makare ba zai samu wannan garabasa ba. Sai dai ba haka ta faru ba.

Rahotannin da su ka zo mana shi ne, fasinjoji shida ne kacal su ka yi amfani da jirgin. A Ranar Litinin, an samu mutum biyu da su ka hau jirgin da yamma daga tashar Iju da ke Garin Legas.

A kashegarin wannan rana (Ranar Talata), an samu karin mutane hudu da su ka shiga jirgin. Duka-duka dai an samu fasinjoji shida a kwana biyu. Jami’ai sun ce su na sa ran jama’a nan gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel