Bidiyo: 'Yan Najeriya na cikin wani hali yayin da 'yan kasar Ghana suka fito da bindigu suka ce fita su bar musu kasarsu

Bidiyo: 'Yan Najeriya na cikin wani hali yayin da 'yan kasar Ghana suka fito da bindigu suka ce fita su bar musu kasarsu

- Xenophobia a kasar Ghana, 'Yan Najeriya sun shiga wani hali yayin da aka fara yi musu barazana da bindiga idan basu bar kasar ba

- Yawaitar hare-haren da ake kaiwa 'yan Najeriya a kasar Ghana, ya fara zama ruwan dare

- Yakamata hukumomin Najeriya su tashi tsaye don kara duba yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen

- Hassada da tsana ce a tsakanin 'yan kasuwar kasar da 'yan Najeriya, duk da dai zamu iya kintata dalilin hare-haren

Yawaitar hare-haren da ake kaiwa 'yan Najeriya a kasar Ghana, ba abun kyalewa bane a wajen hukumomin Najeriya.

Harin kwanakin nan da aka kaiwa 'yan kasuwar Najeriya a Ghana da wasu kasashen Afirka ta Yamma yana bukatar bincike tare da matakin gaggawa daga gwamnatin tarayya. Akwai bukatar a binciko dalilin da ke kawo wadannan hare-haren.

Akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara duba irin shirye-shiryen da ke tsakaninta da wasu kasashen na Afirka. Dole ne manyanmu su tashi tsaye wajen duba al'amuran da ke kawo babbar barazana ga 'yan kasar nan a kasashen ketare.

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda wata mata ta yiwa mijinta dukan tsiya saboda ya kirata da karuwa a bainar jama'a

A tattaunawar da Gistmania ta yi da wadanda abun ya shafa, wani Uchenna wanda dan kasuwa ne a Ghana ya ce: "Akwai bukatar 'yan kasashen ketaren da ke kasarmu su dandana abinda muke dandanawa a kasarsu. Muna karramasu tare da mutuntasu a Najeriya amma mu ana mana kallonmu a matsayin 'yan ta'adda a kasashensu. Harin da ake kai mana shine babban tashin hankalin."

Kamar yadda yake nunawa a bidiyon, 'yan sandan kasar Ghana na harbi, kuma wasu mutanen kasar na lalata motoci da kadarori mallakin 'yan Najeriya.

Zamu iya kintata abinda ya kawo wannan harin, amma rahoto ya nuna cewa, tsana da hassada ce da 'yan kasar Ghana ke wa 'yan Najeriya. Wannan na nuna cewa kaunar juna da ke tsakanin 'yan Afirka duk babu ita a yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel