DSS ta bankado wani makirci da aka shirya haddasawa a yayin bukukuwan karshen shekara

DSS ta bankado wani makirci da aka shirya haddasawa a yayin bukukuwan karshen shekara

Hukumar 'yan sandan farar hula, DSS, a ranar Talata ta sanar da cewa ta gano wata makirci da wata makirci da wasu kungiyoyin bata gari ke shiryawa don janyo tabarbarewar doka da oda a sassan kasar har ma da birnin tarayya, Abuja.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Dakta Peter Afunanya ya fitar, ya ce ana shirin tsara zanga-zanga, tattaki mutane masu yawa tare da rikici da niyyar janyo rashin zaman lafiya a kasar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce an tsara gudanar da tayar da rikicin ne a lokaci guda a wasu manyan birane a yankunan siyasa na kasar cikin 'yan makonni masu zuwa kuma masu shirya makircin suna niyyar janyo rikicin ne lokutan bikin kirsimeti da sabon shekara.

Saboda irin matsalar da wannan makircin zai haifar ga al'ummar kasa da tsaro, ya ce hukumar tana gargadi ga makiya demokradiyar da ke niyyar tayar da rikicin da su yi watsi da shirin da su kayi.

DUBA WANNAN: 'Yar Buhari ta kammala digiri da sakamako mafi daraja daga jami'ar UK

Ya kara da cewa hukumar ta DSS da sauran hukumomin tsaro za su kasance cikin shiri domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a dukkan sassan kasar kafin bukukuwan, yayin bukukuwan da bayan bukukuwan.

Ya yi kira ga sauran al'umma masu biyaya ga doka su cigaba da gudanar da harkokinsu da suka saba ba tare da tsoro ba amma su kai rahoton duk wani mutum ko kungiya da suke zargin yana yunkurin tayar da hankulan al'umma zuwa ofishin hukumomin tsaro mafi kusa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel