Sanatoci 3 da INEC ta sanar da sun fadi zabe amma su kayi nasara a kotu

Sanatoci 3 da INEC ta sanar da sun fadi zabe amma su kayi nasara a kotu

An yi zabubbukan 2019 cike da nasara da rashin hargitsi ko hayaniya. Bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana sakamakon zabe, 'yan takara masu yawa da jam'iyyun siyasa sun garzaya kotu a kan rashin gamsuwa da sakamakon.

Ga wasu sanatocin Najeriya da suka fadi zabe amma suka yi nasara a kotu;

1. Mohammed Musa (Niger)

Kotun koli ta kwace kujerar David Umaru na jam’iyyar APC. Sanata ne mai wakiltar jihar Neja ta gabas. Kotun ta maye gurbinsa da Mohammed Musa na jam’iyyar APC din.

Tun farko dai an mika sunan Umaru David ne a maimakon Mohammed Musa ga INEC, wannan kuskuren kuwa an sameshi ne daga jam’iyyar. Domin kuwa Mohammed Musa ne yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC din a yankin.

Tun daga farko dai, Mohammed Musa ya mika kokensa gaban kotun tarayya saboda rashin gamsuwa da yadda Umaru David ya samu tikitin, alhalin ba shine ya lashe zaben fidda gwani ba. Kotun ta jaddada nasarar Umaru amma sai Musa ya daukaka kara. Kotun daukaka karar itama ta jaddada nasarar David, lamarin da ya kaisu har gaban kotun koli.

DUBA WANNAN: Abubuwa 10 da yakamata a sani game da sabuwar jami'ar sufuri ta Daura

2. Sanata Biodun Olujimi (Ekiti)

Kotun daukaka kara da ke zama a Ado Ekiti, ta bayyana Sanata Biodun Olujimi a matsayin sahihiyar wacce ta lashe zaben kujerar Sanata ta jihar Ekiti ta Kudu.

Kotun daukaka karar ta kwace kujerar Prince Dayo Adeyeye, mai magana da yawun majalisar dattijai inda ta maye gurbinsa da Olujimi. Hukuncin ya soke hukunci kotun sauraron kararrakin zabe.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, ta bayyana Prince Dayo Adeyeye na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, amma kotu ta kwace kujerar tare da ba wa Sanata Biodun Olujimi ta jam’iyyar PDP.

3. Sanata Smart Adeyemi (Kogi)

A halin yanzu shine Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta Yamma. Da farko hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana Sanata Dino Melaye a matsayin wanda ya lashe zaben.

Rashin gamsuwa da hakan ne yasa Adeyemi ya tunkari kotu, inda bayan tafka shari'a aka bukaci maimaita zaben a yankin.

An maimaita zaben a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba 2019 amma sai INEC ta bayyana cewa zaben bai kammalu ba.

A ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba ne aka sake maimaita zaben inda ya yi nasarar maka Sanata Dino Melaye da kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel