Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo Abuja bayan ziyarar da ya kai Malabo da Katsina

Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo Abuja bayan ziyarar da ya kai Malabo da Katsina

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma babban birnin tarayya, Abuja bayan ziyarar aiki na kwanaki biyar da ya kai zuwa Malabo a kasar Equatorial Guinea, Jihar Katsina da kuma jihar Kaduna kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A ranar 28 ga watan Nuwamba ne shugaban kasar ya bar Abuja domin zuwa hallartar taron kasashe masu samar da iskar gas, GECF karo ta 5 da aka gudanar a Malabo.

A jawabinsa a wurin taron, shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa tana daf da fara ginin hanyar bututun gas mai nisan kilomita 600 daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano da zai jigilar gas daga kudancin Najeriya zuwa arewacin kasar.

Shugaban kasar ya kara da cewa akwai yiwuwar kara shimfida bututun gas din zuwa yankin Afirka ta Yamma.

DUBA WANNAN: PDP ta amince da nadin Sanata Nazif a matsayin mataimakin shugabanta na kasa

Shugaba Buhari ya kuma gana da Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea da mataimakin shugaban kasar Iran na harkokin cikin gida Mohammad Nahavandian.

Wadanda suka raka shugaba Buhari taron zuwa Malabo sun hada da Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, Ministan ma'adinai da karafa, Olamilekan Adegbite da babban manaja hukumar kula da man fetur na Najeriya, NNPC, Mele Kolo Kyari.

Shugaban kasar ya bar Malabo a ranar Juma'a bayan kammala taron inda ya wuce Daura a jihar Katsina don wata ziyarar aikin inda ya kaddamar da jami'ar sufuri ta Daura.

Kafin ya koma Abuja, shugaban kasar ya kuma ziyarci jihar Kaduna inda ya kaddamar da motar da nakiya bata iya lalata ta, MRAP na farko da aka kera a Najeriya domin yaki da ta'addanci da wasu ayyukan.

Kamfanin kera makamai ta Najeriya, DICON ce ta kera motar yakin da aka rada wa suna Ezugwu MRAP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel