Atiku ya bayyana mawuyacin halin da hadimar Buhari ta jefa shi ciki

Atiku ya bayyana mawuyacin halin da hadimar Buhari ta jefa shi ciki

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a ranar Talata ya bayyana gaban wajen shigar da kara na babbar kotun tarayya da ke Maitama a Abuja rantsuwa a kan kokensa na cin mutunci da tozarci da hadimar shugaban kasa Buhari ta masa.

Ya bukaci kotun da ta ci tarar N2.5bn da yake so ayi wa hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie a kan laifukan da yake zarginta da su.

Hotunan dan takarar PDP din tare da shugaban lauyoyinsa Chief Mike Ozekhome da sauran lauyoyinsa sun kai ga manema labarai a ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch at ruwaito.

A daya daga cikin hotunan, an ga Atiku na zaune rike da takarda tare da alkalami a kan farar takarda, inda Ozekhome ya rankwafo da kansa a teburin.

A karkashin hoton, Ozekhome ya rubuta: Ozekhome a yau tare da Atiku Abubakar a babbar kotun tarayya da ke Maitama.

DUBA WANNAN: PDP ta amince da nadin Sanata Nazif a matsayin mataimakin shugabanta na kasa

“Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya je da kanshi wajen shigar da karar don saka hannu a kan rantsuwarsa a kan mugun halin da hadimar shugaban kasar ta jefa shi, kuma ya maka ta kotu a kai. Wazirin na bukatar naira biliyan biyu da rabi daga hadimar a kan bacin suna da damuwa da ta jefa shi a ciki.”

A ranar 26 ga watan Yuni ne Atiku Abubakar ya maka Onochie a gaban kotu don kwato masa hakkinsa na bacin sunan da ta yi mishi, sakamakon wallafar da ta yi a shafinta na tuwita na ranar 27 ga watan Mayu.

Wallafar ta bayyana cewa, sunan Atiku na cikin jerin sunayen mutanen da jami'an tsaro ke farauta a daular larabawa ta UAE, kuma ya yi tafiya zuwa gabas ta tsakiya don siyayyar abubuwan da suka danganci ta’addanci.

Ya bukaci kotun da ta umarci Onochie da ta biya shi naira biliyan biyu da rabi sakamakon tozarcin da ta ja mishi, bacin suna, rashin kwanciyar hankali da sauransu, da ta jefa shi ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel